Bikin Sallah: DSS ta Shawarci Masallata Yayin da Ake Shirin Fita Sallar Karamar Idi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Rundunar Tsaro ta farin Kaya DSS ta shawarci musulmi da su sanya ido sosai yayin da suka isa filin idi domin gudanar da sallah da za a fara gobe Laraba.
Rundunar ta shawarci musulmi da su gaggauta mika duk wasu bayanan motsin da ba su aminta da su ba, kamar yadda rahoton daily trust ya nuna.
DSS ta ce musulmi su kwantar da hankalinsu, su kuma gudanar da bukukuwan sallah cikin nutsuwa, domin tuni aka samar da matakan kare rayukansu da dukiyoyinsu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar DSS, Peter Afunanya ya bayyana haka yayin da ake shirin shagulgulan sallah karama.
A kalaman Afunanya:
“Muna shawartar kowa ya sa ido sosai tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani mosti da ba su gamsu da shi ba.”
“A bangarenmu, za mu ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin salama.”
Bayan gaza ganin jaririn watan Shawwal a yammacin Litinin ne dai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ayyana Laraba a matsayin 1 ga watan ƙaramar sallah.
Tun a ranar Lahadi, fadar Sarkin Musulmin ta buƙaci Musulmin Najeriya su fara duban watan Shawwal a yammacin Litinin.
Ranar Sallah dai na daga lokutan da aka fi son musulmi su yi kwalliya da tufafi mai kyau, su yawaita kabbara, su je sallar idi sannan su sada zumunci.
Asali: Legit.ng