Home Back

Tafiyar Karshe da Aminu Ado Bayero Yayi da Bai Sake Shiga Fadar Sarkin Kano ba

legit.ng 2024/6/30
  • A cikin watan Mayun shekarar nan, Aminu Ado Bayero ya kai ziyara wajen Sarkin Ijebu Ode a jihar Ogun
  • Mai Martaban yana can ne majalisar dokokin Kano tayi doka, a karshe aka sauke shi daga sarautar da yake
  • Sarki Aminu Ado Bayero ya tuno da zumuncin da ke tsakanin Mai martaba Awujale da Mahaifinsa Ado Bayero

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ogun - A karshen watan Mayun 2024, Aminu Ado Bayero ya kai ziyara zuwa garin Ijebu-Ode a jihar Ogun domin gaida basaraken kasar.

Mai martaba Sarkin Kano ya na wajen wannan tafiya ya samu labari cewa majalisar dokoki ta ruguza dokar masarautar da ta nada shi.

Sarkin Kano
Aminu Ado Bayero yana Ogun aka canza Sarkin Kano Hoto: @HRHBayero Asali: Facebook

Tafiyar Sarki Aminu Bayero Ogun

Daily Trust ta kawo labarin wannan tafiya da Sarki Aminu Ado Bayero ya yi, kafin ya dawo kuwa Muhammadu Sanusi II ya shiga fadar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Laraba, 22 ga watan Mayu 2024, Aminu Bayero da fadawansa suka isa fadar Mai martaba Sarkin Ijebu Ode da karfe 11:00 na safiya.

Sarkin ya tafi kudu maso yammacin Najeriyan ne domin taya Sarki murnar cika shekara 90.

Kwamishinan masarautu da harkokin kananan hukumomi, Alhaji Ganiyu Hamzat ya wakilci gwamna Dapo Abiodun wajen haduwar.

Sanata Lanre Tejuoso da Wasiu Ayinde Marshal suna fadar a lokacin. Leadership ta ce tun farkon wata aka tsara za a ayi wannan ziyarar.

Kabiyesi ya yabawa Sarki Aminu Ado Bayero

Da ya tashi jawabi, Mai martaba Awujale ya yabawa Aminu Ado Bayero da yadda ya rike zumunci ganin yana cikin abokan mahaifin nasa.

Sarki Aminu Ado Bayero ya ce ya tashi ya ji Mai martaba Ado Bayero yana yawan kiran Kabiyesi Awujale danuwansa, sun shaku sosai.

Alakar Sarkin Kano da Sarkin Ijebu

Baya ga dattijon Sarkin ya dade a mulki kamar mahaifinsa, ya shafe shekaru 64 a karaga, masarautarsa da ta Kano sun yi kama da juna.

Sarki ya ce an san Kano da Ijebu wajen harkokin kasuwanci, a karshe kuma ya yi alkawari zai sake kawo wata ziyara cikin watan Agusta.

Daf da karfe 2:00 na rana Sarki Bayero ya bar fadar Awujale, a can Kano kuwa ana shirin maido Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.

An yi kuskuren nada Sarkin Kano?

An rahoto lauyan nan, Abba Hikima ya ce Abba Kabir Yusuf ya buga katabora a dokar kasa wajen nadin sabon sarki bayan ya rusa masarautu.

Fitaccen lauyan ya ce gwamna ya dogara da rusasshiyar doka a kokarin maido Muhammadu Sanusi II, sai dai wasu sun sabawa lauyan.

Asali: Legit.ng

People are also reading