Home Back

Tinubu Ya Kaddamar Da Gangami Yakin Neman Ilimi

leadership.ng 2024/9/20
Cire Tallafin Mai: Za A Fara Bai Wa Talakawa Dubu 8 Duk Wata

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da gangamin yakin neman bunkasa ilimi da koyon aikin hannu da kuma na daidaiton jinsi.

Gangamin mai taken “Dukkaninmu Daya Muke” kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika (OAFLAD) ce ta gabatar da tsarawa.

 An kaddamar da gangamin a kasashe 15 da ke da manufar bunkasa harkokin kiwon lafiya, ilimi, samar wa mutane ababen dogaro da kai na sana’o’i, da kuma yaki da cin zarafin jinsi.

Nijeriya wacce ta dauki shirin wajen maida hankali kan taken cewa ilimi shi ne babban hanya na kawo canji, wanda matar shugaban kasa Sanata Senator Oluremi Tinubu ta gabatar.

Da yake kaddamar da gangamin a fadar shugaban kasa, Tinubu ya jinjina wa kokarin matan shugabannin kasashen Afrika, da suka kasance masu maida hankali wajen ganin an samu daidaiton jinsi da ke cikin matsalolin da yankin ke fama da shi.

“Wannan gangamin na da matukar muhimmanci a garemu a nan Afrika, don haka, ina tayaku murna, musamman matata Senator Oluremi Tinubu, wacce ta kasance ta zabi bangaren ilimi a matsayin abu na farko da ganganmin zai maida hankali a kansa a fadin kasar nan.

“Manufar kaddamar da wannan gangamin a Nijeriya shi ne, babban hanya na kawo sauyi, muhimmin lamari ne wajen ci gaban Afrika, idan muka samu nasarar wajen daidaiton jinsi da tabbatar da damarmaki ga kowa.

“Dole mu ci gaba da samar da hanyoyi na damarmaki ga dukkanin yaranmu wajen ganin sun samu damar samun ilimi ba tare da barin kowa a baya ba, musamman yara mata.

“Dole ne mu samar da al’umma da babu bambancin jinsi da kowa zai kasance na samun dama kamar kowa, ba tare da la’akari da waye ba, saboda ta hakan za mu iya gina al’umma mai cike da kwanciyar hankali ga kowa,” ya shaida.

 A cewarsa, shirin wani dama ne karo na biyu wajen ganin an rage kaifin matsalar yaran da ba su zuwa makaranta domin ganin sun koma zuwa makaranta wajen tunkarar yadda za su kyautata rayuwarsu na gaba.

Tinubu ya yi alkarin cewa nan ba da jimawa ba ta karkashin hukumar kula da ilimi a matakin farko za a samu nasarar gina wasu makarantu ta yadda za a ci gaba da dakile matsalolin da suke akwai.

People are also reading