Home Back

Summer Davos: An Tattauna “Sababbin Damammaki A Kasar Sin”

leadership.ng 3 days ago
davos

“Gwamnatin Sin ta jadadda inganta sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko cikin sauri, da kuma ci gaba da tsara sabbin hanyoyin samun ci gaba da sabbin fa’ida, tare da ci gaba da aiwatar da manufofin manyan tsare-tsare daban daban, muna da kwarin gwiwa kan hanya da manufofin ci gaban tattalin arziki da aka gabatar. “

Mataimakin shugaban sashen kasar Sin na kamfanin Deloitte, Liu Minghua ne ya bayyana hakan yayin da ya halarci dandalin tattaunawa na Davos na lokacin zafi karo na 15 a jiya Laraba.

Dandalin tattaunawa na Davos na lokacin zafi da aka gudanar a birnin Dalian na kasar Sin daga ranar 25 zuwa na 27 ga watan nan, ya samu halartar masana harkokin siyasa da kasuwanci da ilimi fiye da 1700 daga kasashe da yankuna fiye da 100 na duniya. Yawancin bakin da suka halarci taron sun bayyana cewa, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin tana da karfi, wanda hakan ya sa kamfanoni daga sassan duniya ci gaba da zurfafa shiga kasuwannin kasar.

Bisa jigon “Sabbin iyakokin ci gaba a nan gaba”, taron ya yi nazari kan sabbin hanyoyi da karfin ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda ke nuna kyakkyawar niyyar al’ummar duniya ta neman sabbin damarmakin bunkasuwa ta hanyar hadin gwiwa.

Kasar Sin ta gabatar da wata ajanda mai kunshe da abubuwa hudu, inda ta yi kira da a zurfafa mu’amalar kimiyya da fasaha da hadin gwiwa, da kafa ginshikin samun ci gaba maras gurbata muhalli, da kiyaye yanayin bude kasuwanni, da sa kaimi ga bunkasuwar kasa da kasa, kana ta gabatar da “dabarun kasar Sin” na samun ci gaban tattalin arziki a nan gaba. (Safiyah Ma)

People are also reading