Home Back

Putin ya gargaɗi Koriya ta Kudu kan bai wa Ukraine makamai

bbc.com 2024/7/3

Asalin hoton, Reuters

Vladmir Putin
Bayanan hoto, Koriya ta Kudu ta bai wa Ukraine tallafin kayayyaki da kuma wasu na aikin soji amma zuwa yanzu ba ta ba ta makaman yaƙi ba

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gargaɗi Koriya ta Kudu kan "babban kuskure" idan ta sake ta aika wa Ukraine makamai a yaƙin da take yi da Rashar.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan Seoul ta ce tana duba yiwuwar yin hakan a matsayin martani ga yarjejeniyar tsaro da Rashar ta ƙulla da Koriya ta Arewa domin taimaka wa juna idan wata ƙasa ta kai wa ɗayarsu hari.

Moscow "za ta...[ɗauki] matakin da ba lallai ya yi wa shugabannin Koriya ta Kudu daɗi ba" idan ta bai wa Ukraine makamai, kamar yadda Mista Putin ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis.

Shugaban na Rasha na magana ne a Vietnam jim kaɗan bayan ziyarar da ya kai Pyongyang babban birnin Koriya ta Arewa, inda suka saka hannu kan yarjejeniyar tare da Shugaba Kim Jong Un.

Putin ya kuma yi gargaɗin cewa Rasha za ta bai wa Koriya ta Arewa makamai idan Amurka da ƙawayenta suka ci gaba da bai wa Ukraine makamai.

"Waɗanda suke bayar da waɗannan makaman suna tunanin cewa ba yaƙi suke yi da mu ba. Na faɗa cewa baya ga Koriya ta Arewa, muna da 'yancin tura makamai zuwa sassan duniya," a cewar Putin.

Tun da farko Koriya ta Kudu ta yi tir da yarejejniyar da ƙasashen suka ƙulla a matsayin wata barazana ga tsaron ƙasarta, har ma mai ba da shawara kan tsaro Chang Ho-jin ya ce ƙasarsa na shirin "duba bai wa Ukraine makamai".

Bayan kalaman na Putin, ofishin shugaban ƙasar ya ce za su "duba hanyoyin da za su iya" bai wa Ukraine makaman kuma "matsayarta za ta dogara ne da yadda Rasha ta ɓullowa lamarin".

Ta kuma yi wa jakadan Rasha Georgy Zinoviev sammaci don nuna ɓacin ranta, tana mai neman Rasha "ta gaggauta jingine ƙawancen soji da Koriya ta Arewa".

Yayin da Koriya ta Kudu ta bai wa Ukraine tallafin kayayyaki da kuma was kayan aikin soji, zuwa yanzu ba ta ba ta makaman yaƙi ba sakamakon tsarinta na ƙin bai wa wata ƙasa makamai matuƙar tana cikin yaƙi.

Yayin ziyarar, Mista Kim ya bayyana "cikakken goyon bayansa" ga mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine. Akwai hujjoji masu ƙwari da ke nuna tuni Rashar ta fara amfani da makaman Koriyar a kan Ukraine.

A ranar Juma'a mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Amurka John Kirby ya magantu kan yarjejeniyar tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa, yana mai cewa "abin damuwa ne ga duk wata ƙasa da ke son zama lafiya" a yankin.

Japan ta ce "ta damu matuƙa game da yadda Putin bai cire maganar taimaka wa Koriyar da fasahar ƙera makamai ba" a yarjejeniyar, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ƙasar Yoshimasa Hayashi ya bayyana.

Masu sharhi na cewa yarjejeniyar za ta iya yin tasiri mai girma a kan sauran ƙasashe, musamman ma na yankin. Baya ga yiwuwar Koriya za ta iya bai wa Rasha makamai a fili, za kuma a iya ganin Rashar ta shiga duk wani rikici da zai faru nan gaba tsakanin Koriyoyin biyu.

Har yanzu ana ganin ƙasashen na cikin yaƙi da juna a fakaice, inda suka jibge dakaru ɗauke da makamai a kan iyakokinsu har ma a 'yan kwanakin nan lamarin ya yi ƙamari.

A wani lamarin daban a ranar Alhamis, dakarun Arewa sun tsallaka iyakar Kudu "na ɗan lokaci" kuma suka koma bayan dakarun Kudun sun yi harbin gargaɗi, a cewar hukumomin Kudun ranar Juma'a.

Wannan ne karo na uku da aka samu irin hakan cikin ƙasa da mako uku. Hukumomin Kudu sun ce lamarran biyu na baya - a ranar 9 da kuma 18 ga watan Yuni - ba da gangan ba ne.

People are also reading