Home Back

Sojojin Sama Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 100, ‘Yansanda Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace A Katsina

leadership.ng 2024/7/1
Sojojin Sama Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 100, ‘Yansanda Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace A Katsina

Rundunar sojin saman Nijeriya, ta sake kashe ‘yan ta’adda sama da 100 a wani sumame da ta kai da daddare a sansanin Kuka Shidda, da ke karamar hukumar Faskari, a jihar Katsina.

Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji, ne suka kai farmakin kan wata kungiyar masu aikata miyagun laifuka da ke da alaƙa da fitaccen sarkin ‘yan ta’adda, Yusuf Yellow, da kuma na hannun damarsa Rabe Imani.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula, ya fitar ya ce sun lalata sama da babura 45 a yayin harin da jiragensu, inda ya ce wannan shi ne karo na uku da sojojin saman Nijeriya, suka samu nasarar kai farmaki a yankin Faskari-Kankara, na jihar kwanan nan, wanda ya kawo cikas ga ayyukan ‘yan bindigar a yankin.

Kaula, ya kuma kara da cewa daukin gaggawar da jami’an tsaron suka yi ya dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane da sanyin safiyar Lahadi, a karamar hukumar Jibia ta jihar, lamarin da ya kai ga ceto mutane uku.

Sanarwar ta kara da cewa, matakin gaggawar ba kawai ceton rayuka ba ne, har ma da aike sako mai karfi ga masu aikata laifuka cewa ba za a lamunci irin wannan aika-aikar ba, wanda ya ce nasara da su ka samu ta na nuna irin jajircewar da rundunar sojin sama da sauran jami’an tsaro na kananan hukumomi ke yi wajen kare rayuka da dukiyar al’ummar Jihar Katsina.

People are also reading