Home Back

Real Madrid za ta fara La Liga 2024/25 da zuwa gidan Mallorca

bbc.com 2024/7/7
La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid za ta fara gasar La Liga ta 2024-25 da kai ziyara gidan Real Mallorca a karshen makon 17 ko kuma 18 ga watan Agusta.

Kamar yadda mahukuntan babbar gasar tamaula ta Sifaniya suka fitar da jadawalin kakar da za a fara cikin watan Agusta, bayan da Real Madrid ke rike da kofin bara.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta karkare karawar karshe a Santiago Bernabeu da Real Sociedad a karshen makon 24 ko 25 ga watan Mayun 2025.

Za a fara yin wasan hamayya na El Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona a Santiago Bernabeu a mako na 11 ranar 26 ko 27 ga watan Oktoba.

Wasa na biyu kuwa za a yi ne tsakanin 10 ko kuma 11 ga watan Mayun 2025 a Barcelona karawar mako na 35.

Haka kuma Real za ta buga fafatawar hamayya ta birnin Madrid da Atletico a mako na takwas ranar 28 ko kuma 29 ga watan Satumba.

Filin Santiago Bernabeu zai karbi bakuncin wasa na biyu na hamayya na birnin Madrid da Atletico a mako na 23 ranar 8 ko kuma 9 ga watan Fabrairun 2025.

Real Madrid ce ta lashe La Liga da aka kammala na 2024/25 kuma na 36 jimilla, sannan ta dauki Champions League na 15 jimilla.

Jadawalin wasannin makon farko

  • Athletic Bilbao da Getafe
  • Real Betis da Girona
  • Celta de Vigo da Deportivo Alaves
  • Real Mallorca da Real Madrid
  • Osasuna da Leganes
  • Real Sociedad da Rayo Vallecano
  • Valencia da FC Barcelona
  • Villarreal da Atletico Madrid
  • Las Palmas da Sevilla
People are also reading