Home Back

Fatima Alkali: Ɗalibar da Ta Rikita Arewa Bayan Samun Maki 366 a Jarabawar UTME

legit.ng 2024/5/17
  • Yayin da hukumar JAMB ta sake sakamakon jarrabawar UTME, wata daliba 'yar Arewa ta burge 'yan Najeriya
  • Dalibar mai suna Fatima Saleh Alkali ta samu maki 366 a jarrabawar da aka gudanar wanda mafi yawa suka fadi
  • Wannan na zuwa ne bayan sake sakamakon inda hukumar ta ce 76% daga cikin daliban sun samu maki kasa da 200

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe - Wata daliba mai suna Fatima Saleh Alkali ta burge mutanan Najeriya bayan fitar da sakamakon jarrabawar UTME a bana.

Fatima ta samu maki 336 a jarrabawar ta bana duk da yawan faduwa da aka samu daga ɗalibai.

Wani mai amfani da kafar X, Dakta Yakubu Sani Wadil shi ya wallafa haka a yau Alhamis 2 ga watan Mayu.

Wudil ya ce ya kamata a yi kira ga Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bata tallafin karatu har zuwa matakin digirin-digirgir.

Ya ce tabbas za ta daga darajar jihar a idon duniya idan aka mara mata baya wurin ɗaukar nauyin karatunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibar ta samu maki 68 a Turanci sai kuma 93 a darasin lissafi da maki 87 a Physics sai kuma 88 a Chemistry.

"Wannar daliba ce daga Arewacin Najeriya, Fatima Saleh Alkali, ta samu maki 366 a jarrabawar UTME duk da yawan faduwa da aka yi."
"Ya kamata mu hada hannu domin yin kira ga gwamnan jihar Yobe ya dauki nauyin karatunta har matakin PhD, za ta daga sunan jihar Yobe idan aka ɗauki nauyinta yadda ya kamata."

- Dakta Yakubu Wudil

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading