Home Back

GMF 2024: Babban taron 'yan Jaridu na duniya

dw.com 2024/7/6
GMF 2024 | Tasirin dimukuradiyya | tare da Annalena Baerbock

Tuni dai 'yan jarida 1000 da sauran masu ruwa da tsaki suka fara muhawa kan taken taron na bana kan musayar bayanai domin samun mafita. hoto.

Taron ya hada 'yan jarida daga sassa daban-daban na duniya karo na 17 wanda ya mayar da hankali kan yadda za a yi musayar mafita domin tunkarar irin matsalolin da duniya ta fada musamman rikice-rikicen da wasu yankunan ke fama da su.

Karin Bayani: Taron 'yan jaridu na DW bayan corona

A jawabinsa na bude taron, babban daraktan tashar DW Peter Limbourg ya jadadda cewa, ko wane rikici da ake fuskanta a duniya 'yan jarida na taka mahimmiyar rawa wajen bayar da bayanai da sharhi kan lamarin da kuma tabbatar da sahihancin labari domin haka ne ya ce musayar bayanai domin samun mafita shi ne dabarun da za a yi amfani da su a yanzu.

''Mr. Limbourg ya ce ina muku maraba da zuwa taron daga sassa daban-daban na duniya. Muna kuma mika godiya ga masu daukar nayin taron. Ina matukar farin cikin da taken taron na bana, wato musayar ra'ayi don samun mafita. A lokacin da ake tsaka da fuskantar kalubale, musayar mafitar ita ce dabarar da za mu yi amfani da ita a tsakaninmu.''

Karin Bayani: 'Yan jarida na Ukraine sun samu kyautar DW

A nasa jawabin da gabatar ta faifan bidiyo da ya aiko wa taron, Firimiyan jihar North Rhein Westphalia, Hendrik Wüst,  ya yabawa 'yan jarida kan kwararru a fannin kan ayyukan da suke gabatarwa da kuma yadda suke sadaukar da rayukansu domin bayar da sahihan bayanai ga al'umma. Ya kuma ce akwai bukatar a bayan da muhimmanci kan  'yancin fadin albarkacin baki da ma 'yancin 'yan jarida a duniya.

Ya ce "dukannin 'yan jarida na duniya na tsayin daka a kullum, a wasu lokutan ma rayukansu na cikin hadari. A nan Jamus muna da'awar yaki da labarai na bangaranci, sai dai kuma masu tsattsauran ra'ayi na adawa da 'yancin aikin jarida da ma kafafen rediyo, suna kuma dogara a kan labarai na kazon kurege da yada manufa har ma da kalan tuzura, kuma dole mu nuna adawa da manufofinsu."

Karin Bayani: DW: Taron 'yan jaridu na shekara-shekara

Daga cikin abubuwan da aka mayar da hankali a kansu a farkon zangon taron shi ne yadda ake gudanar da ayyukan jarida a sassa daban-daban. Sai dai kuma masana sun jadadda cewa bukatar yin adalci ga kowane bangare na yada labari da kuma samar da mafita shi ne mai mahimmanci idana aka kwatanta da saran sassa na yada labaru, kamar yadda Ellen Heinrichs ta cibiyar aikin jarida ta Bonn Institut ta shaida.

Ta ce "a ganina, yin aikin jarida ta hanyar samar da mafita na da matukar mahimmanci, wanda ya hada da fitar da matsalolin fili don samar da mafita. Aikin har wa yau na samar da muhawara da nufin samun mafita ga batutuwan da ake bukatar a yada wa jama'a, sannan ya na bada dama a bugi jaki a kuma buki taiki da kuma daga muryoyi da dama"

A yanzu haka, masana da 'yan jarida na ci gaba da muhawara inda za a kwashe tsawon yinin yau da ma gobe Talata  ana musayar bayani kan samun mafita game da batutuwan da suka yi wa duniya dabaibayi.))

People are also reading