Home Back

El-Rufai ya maida wa majalisar Kaduna martani, ya ce dama kitsa musu aka yi su ci masa mutunci, amma ‘na gaba ya yi gaba’

premiumtimesng.com 2024/7/3
Tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkin Jama’a ya sha kaye a shari’ar sa da El-Rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta aikata ba daidai ba a lokacin da yake mulkin jihar Kaduna, sannan kuma zargi ƴan majalisar dokokin jihar da gudanar da binciken kiyayya ga mulkin sa ba wai don an aikata laifi ba.

A wata sanarwa wacce kakakin tsohon gwamnan ta fitar ranar Laraba ya ce abinda majalisa ta yi wasan kwaikwayo nean kitsa musu abinda za su ce tun farko.

” Muna da labari cewa Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da rahoton kwamitin wucin gadi da ta nemi a binciki gwamnatin El-Rufai. Ba a ba mu kwafin rahoton ba, wanda za mu mayar da martani sosai a duk lokacin da muka samu.

” Mun tabbatar da sahihancin gwamnatin El-Rufai tare da yin watsi da badakalar da ake yadawa a matsayin rahoton kwamitin.

” Nasir El-Rufai yana matukar alfahari da irin nasarorin da ya samu a harkar mulki da irin abubuwan da ya bari a jihar Kaduna. Bita da ƙullin da ake yi masa ta hanyar amfani da majalisar jihar ba za ta yi tasiri ba ko kadan.

” Kusan duka waɗanda kwamitin binciken ta bukaci su bayyana a gabanta sun bayyana, kuma tun a wurin sinbsan kawai wasan kwaikwayo ne a ke yi an shirya yadda za a ƙarkare zaman holoƙo a kayi.

” Muna so mu tabbatar muku cewa El-Rufai ya yi aikin tukuru domin mutanen Kaduna kuma su da kansu mutanen jihar sun shaida. Ayyuka akayi facafaca a jihar babu kama hannun yaro.

A karshe sanarwar ta yi kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankalansu cewa abinda ake kullawa ba za ta kullu ba domin yana da gaskiya a duka abinda aka yi a jihar kuma an bi doka da oda alokacin da ake ayyukan rayawa da gyara jihar.

People are also reading