An Mikawa Gwamnatin Zamfara 'Yan Mata da Samarin da Aka Ceto a Hannun 'Yan Bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta mika mutanen da aka sace a jihar Zamfara ga jami'an gwamantin jihar.
A yau Alhamis ne aka mika mutanen bayan an ceto su daga hannun yan bindiga a ranar 27 ga watan Yuni.
Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa manyan jami'an gwamnatin jihar Zamfara ne suka karbe su a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya mika matane 16 da ake ceto daga hannun masu garkuwa da mutane.
An ceto mutanen wadanda suka hada da maza takwas da mata takwas ne a ƙananan hukumomin Tsafe da Shinkafi.
A yayin mika mutanen, gwamantin tarayya ta ce za ta cigaba da ƙoƙarin yaki da masu garkuwa da mutane a Najeriya.
Saboda haka ta bukaci yan Najeriya da su rika sanar da jami'an tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Nakwada ne ya jagoranci karbar mutanen a Abuja, rahoton Leadership.
A cikin tawagar har ila yau akwai kwamishinan zartar da ayyuka na jihar Zamfara, Alhaji Zurumi Nasiru.
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun kai wasu sababbin hare-haren ta'addanci a Zamfara wacce ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum takwas a wani sabon hari da suka kai a garin Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.
Asali: Legit.ng