'Yan Bindiga Sun Hallaka 'Yan Gudun Hijira Bayan Sun Raba Su da Gidajensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne ɗauke da makamai sun kashe mutane uku a jihar Benue.
Mutanen dai waɗanda ke rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira na Agagbe sun rasa rayukansu ne lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.
Ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da suke dawowa daga gona.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon manajan sansanin ƴan gudun hijiran, Terna Jacob, ya tabbatarwa da wakilin jaridar The Punch aukuwar lamarin a ranar Talata.
"Sun rasa rayukansu ne yayin da suke dawowa daga gona zuwa makwancinsu a garin Agagbe domin makiyaya sun ƙona musu gidajensu."
- Terna Jacob
Ya bayyana sunayensu a matsayin Mista Ameeya Solomom mai shekara 38 na ƙauyen Tse Kuan a gundumar Mbabuande, Adagu Terwase mai shekara 40 na ƙauyen Tse Abu da Orkaha Terkende mai shekara 16 na ƙauyen Tse Maihwa.
Wakilin jaridar ya tattaro cewa an binne biyu daga cikin waɗanda suka mutu yayin da aka ajiye gawar mutum na ukun a ɗakin ajiye gawa na Agagbe.
Legit Hausa tuntubi jami’ar hulɗa da jama’a ta ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, wacce ta ce ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.
"Ban samu rahoton faruwar lamarin ba."
- SP Catherine Anene
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka wasu manoma mutum huɗu yayin da suke aiki a gonakinsu a wani harin ta'addanci a jihar Katsina.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne a ƙaramar hukumar Jibia mai fama da matsalar rashin tsaro a jihar.
Asali: Legit.ng