Ana Tsaka da Rigimar Sauratar Kano, Fitaccen Basarake Ya Mutu a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya tura sakon ta'aziyya bayan rasuwar fitaccen basarake a Kudancin jihar.
Gwamnan ya jajantawa Agwam Tagwai Sambo da ke sarautar Moro’a Asholyio da ke Manchok a karamar hukumar Kaura.
Uba Sani ya bayyana haka ne a daren jiya Juma'a 14 ga watan Yuni a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Cikin alhini da mika lamura ga ubangji, mun samu labarin rasuwar basarakenmu mai daraja wanda ya ke son zaman lafiya, Cif Agwam Tagwai Sambo da ke Moro’a Asholyio a Manchok."
"Ya jagoranci mutanensa cikin hikima da jarumta da kuma tausayi, ya tsaya tsayin daka wurin tabbatar da adalci tare da inganta al'ummarsa."
"A madadina da iyalaina da kuma al'ummar jihar Kaduna, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin tare yi masa addu'ar samun rahama."
- Uba Sani
Basaraken mai shekaru 87 wanda aka bayyana da mutum mai son jama'a da kuma ci gaban yankinsa ya rasu ne bayan fama da jinya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa basaraken ya kasance mai son ci gaban al'umma da kuma zaman lafiya.
A wani labarin, kun ji cewa kotu ta dawo da basaraken da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya tuge a jihar.
Tsohon gwamnan ya dauki wannan matakin ne lokacin da ya ke jagorantar jihar ana saura kwanaki bakwai ya bar kujerar mulkin jihar.
El-Rufai ya cire Sarkin ne bayan barkewar wani rikici da ya yi ajalin wasu mutane da ake zargin akwai sakacin basaraken.
Asali: Legit.ng