Home Back

Dan a Mutun Tinubu Ya Gindaya Sharudan Raba Gari da Shi, Ya Fadi Alaƙarsa da Atiku

legit.ng 2024/9/28
  • Daniel Bwala ya bayyana abubuwan da za su saka shi raba gari da Shugaba Bola Tinubu bayan kasancewa tare dashi
  • Sai dai ya ce da za ran ya fahimci Tinubu ya kauce hanya to dole su raba gari tun da a mulkin dimukradiyya ake yanzu
  • Bwala wanda tsohon hadimin Atiku ne ya bayyana cewa ya fara goyon bayan Tinubu ne saboda bin dokoki da kuma dimukradiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin Atiku Abubakar, Daniel Bwala ya yi magana kan goyon bayansa ga Bola Tinubu.

Ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan Tinubu saboda tsare-tsarensa da kuma nufin alheri ga Najeriya.

Bwala ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Arise a jiya Laraba 5 ga watan Yuni a birnin Abuja.

Sai dai ya de idan har Tinubu ya kauce tsarin bin dokokin kundin tsarin tarin mulki to a nan ne za su raba gari.

Tsohon hadimin ya bayyana yadda ya goyi bayan Atiku a baya amma yanzu yana tare da Tinubu tun bayan kammala zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lokacin da nake tare da Atiku na ba shi dukkan goyon baya, amma yanzu na dawo tare da Tinubu tun bayan kammala zabe."
"Babban abin da zai saka ni watsar da Tinubu shi ne idan ya fara kauce hanyar bin dokokin tsarin mulki da kuma dimukradiyya."
"Sai dai banga alamomin haka daga gare shi ba saboda har yanzu yana kan hanya mai kyau."

- Daniel Bwala

Bwala ya magantu kan karin albashin ma'aikata

A wani labarin, kun ji cewa Daniel Bwala ya bayyana mafi ƙarancin albashin da ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata.

Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kasance N250,000.

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ƴan jaridu kan yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara.

Asali: Legit.ng

People are also reading