Home Back

An Kashe Mutane 5000, An Sace 7000 Cikin Shekara 1 A Mulkin Tinubu – Bincike

leadership.ng 2024/7/1
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

Wani bincike da kafafen yada labarun Nijeriya da kungiyoyi suka gudanar ya nuna cewa ayyukan ta’addanci sun hallaka mutane 4,500 yayin da aka yi garkuwa da mutane 7,000 cikin shekara guda a karkashin mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ACLED mai tattara kididdigar kisa ko kuma mutanen da aka yi garkuwa da su ta ce bayananta sun nuna cewa mutane 4,556 ne suka rasa rayukansu sai wasu 7,086 da aka yi garkuwa da su a tsakanin ranakun 29 ga watan Mayun bara zuwa 11 ga watan Mayun da muke ciki.

A lokacin jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun 2023 lokacin da aka rantsar da shi, Tinubu ya sha alwashin tunkarar matsalolin ta’addanci da kuma rashin tsaro gadan-gadan.

Wannan ba shi ne karon farko da shugaban ke yi wa ‘yan Nijeriya alkawari kan magance matsalar tsaro ba.

Hakan ya kasance tamkar waka a manyan batutuwan da yake nanatawa a wajen yakin neman zabe.

Sai dai, shekara daya yau cif da darewarsa karagar mulki, a iya cewa babu wani sauyi na azo a gani a bangaren tsaro, illa ma dai sake sabon salon kai hare-hare da ‘yan bindiga musamman a Arewacin kasar nan ke kai wa.

Ita kuwa kungiyar Boko Haram tsagin Ansaru ke ci gaba da samun karfi tare da kai hare-hare a yankin Arewa Maso Gabas.

Cikin makon da ya gabata sai da mahara suka yi garkuwa da mutane 160 a Jihar Neja, a wani hari da ba a taba ganin irinsa a jihar ba.

Duk da alkawuran da shugaban ya yi, da kuma ikirarin yaki da ta’addanci da manyan hafsoshin tsaron kasar ke yi na yaki da ta’addanci, har yanzu matsalolin rashin tsaro na ci gaba da zama ruwan dare.

People are also reading