Home Back

Nijar da Wasu Ƙasashen Afrika Sun Sha Wutan $51m, Sun Ki Biyan Najeriya Kudin Lantarki

legit.ng 2024/7/3
  • Hukumar kula da hasken wutar lantarki ta bayyana cewa kasashen ketare uku ne suka bi biyanta $51.26m na kudin wutar da suka sha
  • A rahoton da hukumar ta fitar, ta ce kasashen Togo, Benin da Niger sun ki biyan kudin wutar da kasar nan ke basu a shekarar 2023
  • Wannan korafi na hukumar na zuwa ne yayin da su 'yan Najeriya ke fama da matsalar rashin wuta, da karin farashinta a kwanakin baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce abokan huldarsa a kasashen ketare sun hana su kuɗin wutar da suka sha.

Hukumar ta ce akalla $51.26m take bin wadanda suka sha wutar a kasashen Niger, Togo da Benin.

Hasken wuta
Kasashen ketare sun ki biyan Najeriya kudin wutar da aka basu Hoto: Daniel Balakov Asali: Getty Images

The Cable ta wallafa cewa wannan bashi ne da take bin kasashen a 2023, wanda kawo wannan lokaci ba a biya ko kwabo daga ciki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NERC ta nemi a dauki mataki

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya ta bayyana bukatar hukumomi su dauki matakin ki kakkabe halayyar kin biyan r

Ta ce abokan huldata sun rabu aji-aji, inda daya daga ciki ya ki biyan bashin N7.61b a 2023, kamar yadda thisradio now ya wallafa.

NERC ta koka kan yadda abokan huldarta suka ki biyan $16.11m a farkon 2023, yayin da aji na biyu na kwastomomin ya ki biyan N827m.

A rahoton da hukumar ta fitar, a rubu'i na biyu na shekarar 2023, kasashen sun ki biyan bashin $11.97m, su kuma aji na biyu sun ci bashin N2b.

NERC ta magantu kan tallafin wuta

A baya mun ruwaito muku cewa hukumar kula da hasken wutar lantarki ta kasa, NERC ta bayyana cewa basu da tabbacin za a iya dawo da tallafin kudin.

Shugaban hukumar kula da wutar lantarki na kasa, Garba Musa wanda ya bayyana hakan ya ce har yanzu ana bin gwamnatin bashin kudi masu tarin yawa na tallafi.

Asali: Legit.ng

People are also reading