Home Back

Direban tasin Birtaniya da ke karɓar albashin aikin gwamnati a Najeriya

bbc.com 4 days ago
A man sits in a stationary vehicle in front of a steering wheel holding a cup of coffee in one hand and a phone in the other

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Mansur Abubakar
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kano

A duk lokacin da ka ajiye aiki, abu na farko da ake sa ran faruwa da kai shi ne daina samun albashi daga wajen aikin da ka bari, amma ba haka abin yake ba ga ma'aikatan gwamnati da dama a Najeriya.

Suna samun aiki a wasu wurare na daban, wani lokaci ma a ƙasashen waje kuma duk da haka suna ci gaba da karɓar albashi daga tsohon wajen aikin nasu.

Labarin irin wannan yanayi ya yi ƙamari ta yadda sai da ta kai ga a makon jiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike da kuma kawo ƙarshen wannan matsala.

Shugaban ƙasar ya ce: “Dole ne a tilasta wa duk masu hannu a wannan yaudara su dawo da duk kuɗin da suka karɓa.”

Wani mutum da zamu kira Sabitu Adams domin ɓoye asalin sunansa, bai ajiye aikin da yake yi a Najeriya ba, a matsayin ƙaramin ma'aikacin gwamnati, domin haka shekara biyu kenan yana samun albashinsa kowanne wata, duk da cewa ya riga ya bar ƙasar.

Yanzu haka yana aiki ne a matsayin direban tasi a Birtaniya, amma ya shaida wa BBC cewa baya da wata fargabar yin asarar albashin da yake karɓa a Najeriya, domin a cewarsa umarnin na Shugaba Tinubu ba komai ba ne illa barazanar fatar baka.

Mr Adams ya ƙara da cewa ba zai ji komai ba idan ya yi asarar albashinsa na Najeriya wanda ya kai naira 150,000, wato dala 100 ko kuma fan 80 kenan, saboda a cewarsa yana samun fiye da hakan a matsayin direban tasi.

“Lokacin da na ji umarnin da shugaban ƙasar ya bayar, sai kawai na yi dariya saboda ina sane cewa abin da nake samu a nan ya zarce na gida Najeriya. Ko kaɗan ban damu ba,” in ji Adams mai shekara 36.

Amma mai ya hana ka shaida wa ma'aikatar da kake aiki a hukumance cewa ka daina aikin?

“Maganar gaskiya na ƙi sanar da su bana nan ne saboda ina tunanin idan zamana bai ɗore ba a nan, zan iya komawa in ci gaba da aikina a Najeriya.”

Asalin hoton, AFP

Nigeria President Bola Tinubu, wearing a blue gown and hat, waves as he arrives for the closing session of the New Global Financial Pact Summit, on June 23, 2023 in Paris
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bincike da kuma hukunta masu karɓar albashi kuma basu yin aiki

Kamar Mr Adams, akwai ƴan Najeriya fiye da miliyan uku da dubu ɗari shida da ke zaune a ƙasashen waje, waɗanda kuma sun shafe fiye da shekara biyu suna can, kamar yadda alƙalumma suka nuna.

Matasan ƙasar da dama ba su ganin cewa za su iya cimma burinsu na rayuwa a cikin ƙasar, wadda ke fama da matsalar taɓarɓarewar darajar naira, da kuma tsare-tsaren da Mr Tinubu yake ɓullowa da su tun da ya zama shugaban ƙasa.

Ya zamo ɗabi'ar matasan ƙasar su nemi tsallakewa domin neman rayuwa mai inganci a ƙasashen waje, har ma sun yi wa irin wannan tafiya laƙabi da ''japa''.

Kalma Yarabancin ce da ke nufin tsira ko tsallakewa.

Mr Tinubu ya ce: "Na kaɗu da kalaman shugabar ma'aikatan gwamnati cewa akwai ma'aikatan da suka tsallake zuwa ƙasashen waje kuma duk da haka ana ci gaba da biyansu albashi kowanne wata".

Shugaban ƙasar ya ce dole ne a ƙwato kuɗin da mutanen suka karɓa, kuma a gudanar da bincike domin ganowa da kuma hukunta duk masu hannu a ciki.

Ya ce “Dole a hukunta dukkan shugabanni da masu kula da ma'aikatu da hukumomin da aka samu irin wannan badaƙala.”.

Kuma wannan na iya zama matsala ga Mr Adams.

Direban tasin da ke aiki a Birtaniya ya shaida wa BBC cewa yana ci gaba da karɓar albashin nasa ne saboda taimakon wasu jami'ai a wajen aikinshi: ''Ina da kyakkyawar alaƙa da maigidana a wajen aiki domin haka ya ba ni damar tafiya babu wata matsala''

Mafi yawa dai ana ƙulla yarjejeniya ne tsakanin ma'aikacin da ke son tafiya da kuma shugabanninsa ko kuma masu lura da shi a wajen aiki, kuma ana raba albashin ne a tsakaninsu.

Amma ga Mr Adams, abin ya zo cikin sauƙi kamar yadda ya ce: "Ban samu wata matsala ba saboda maigidana a wajen aiki ɗan uwana ne na jini."

Asalin hoton, AFP

A market vendor with painted nails counts naira in south-eastern Nigeria - 2023
Bayanan hoto, Faɗuwar darajar naira ya na tilastawa matasan Najeriya da dama fita ƙasashen wajen domin neman ayyukan yi

Ma'aikatan bogi babbar matsala ce a Najeriya. Duk da matakai da ake ta ɗauka domin kawar da ita, ana ci gaba da samun dubban ma'aikatan na bogi da ake biya albashi, ko kuma wasu ke handame albashin nasu. Da alama kuma ba a ɗaukar wasu ƙwararan matakai a kai.

Amma wannan ne karon farko da aka fallasa cewa akwai mutane da yawa da suka bar ƙasar kuma ana ci gaba da biyansu albashi.

Auwal Yakasai, wanda ya yi aikin gwamnati na tsawon shekara 32 ya shaida wa BBC cewa: ''Maganar gaskiya ban taɓa kama kowa ba''

“Amma na samu labarai da yawa game da irin wannan yarjejeniya, inda mutum zai ci gaba da karɓar albashi duk da cewa ya daina aikin ko kuma ya koma wani waje da aiki.”

Tun da ya hau mulki a bara, Mr Tinubu ya sha alwashin rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

A watan Janairu ya bayar da umarnin rage duk wata tawagar tafiyarsa, da ta sauran jami'an gwamnati da kashi 6o cikin dari, wannan kuma ya shafi tafiyar cikin gida da ta ƙasashen waje.

Sai dai kuma akwai masu ganin cewa gwamnatin Tinubun ta cika surutu babu cikawa.

Masu wannan ra'ayi sun kafa hujja da shirin gwamnatin na kashe miliyoyin dala wajen sayen jiragen sama ga Mr Tinubu da mataimakin sa, Kashim Shettim.

Wani abin da suke kafa hujja da shi shi ne yadda a farkon watan nan Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon gidan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a birnin Abuja wanda aka kashe wa kuɗi har naira13.6m.

Kuma duk da cewa shugaban ƙasar ya yi magana a kan ma'aikatan bogi da suke a ƙasashen waje, bai faɗi matakin da yake shirin ɗauka a kan masu hannu a badaƙalar ba.

A woman looking at her mobile phone and the graphic BBC News Africa

Asalin hoton, Getty Images/BBC

People are also reading