Home Back

Gwamnan Zamfara ya musanta ciyo bashin naira biliyan 14.26 da DMO ta wallafa

premiumtimesng.com 2024/5/6
Gwamna Lawal na Zamfara bai kashe Naira miliyan 400  wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje Ba – Fadar Gwamnati

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya musanta cewa gwamnatinsa ta karbo bashin kudi naira biliyan 14.26.

Gwamnan ya kara da cewa kudaden da ake magana a kai na daga cikin rancen naira biliyan 20 da gwamnatin da ta shude ta ciwo tun a baya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya fitar, ta bayyana cewa babu rancen kuɗi da gwamnatin jihar ta karbo a cikin gida ko daga kasashen waje.

“Muna son yin karin haske kan rahoton ofishin kula da basussuka (DMO) da ta wallafa cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.

“Gwamnatin mu ba tun rantsar da ita ba ta taba amsar bashi daga ko ina ba ko tuntubar majalisar jiha ko ta kasa domin bata dama ta ciyo ta bashi a gida ko a waje ba.

” Ina so a sani cewa gwamnatin da ta shuɗe ce ta amshi waɗannan kuɗaɗe kuma ciki ta karbi naira biliyan 4 wato cikin naira biliyan 20.

” Naira biliyan 14 da suka rage cikin kuɗin da gwamnatin da muka gada ta ciyo. Kuma kuɗin na nan ajiye ba a taɓa su ba. Za a yi amfani da su wajen gina filin jirgin saman kamar yadda aka yi niyya.

People are also reading