Home Back

Kotu tayi hukunci akan masarautar Kano

dalafmkano.com 2024/6/29

Babbar kotun tarayya mai zaman ta a Gyadi-gyadi da ke jihar Kano, ta bayyana matsayarta akan a karar da Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar

gabanta akan batun rushe dokar masarautu ta shekarar 2019.

Tun da garko mai kara Aminu Babba Dan Agundi ya yi karar gwamnatin jihar Kano, da majalisar dokokin jihar Kano, inda ya bayyanawa kotun cewar rushe dokar da majalisa ta yi an tauye masa hakkin sa.

Sai dai lauyoyin waɗanda akayi karar sun bayyana wa kotun cewar Aminu Babba Dan Agundi, bashi da wani hakki da majalisar ta tauye masa, sun kuma bayyanawa kotun cewar bata da hurumin sauraron shari’ar masarautu dan haka suka roki kotun da ta yi watsi da karar.

Yayin da ya ke bayyana matsayar sa a yau Alhamis, mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya ce ya soke nadin da akayi wa Muhammadu Sunusi
na biyu, amma hakan bai shafi dokar da majalisar ta yi wa gyaran fuska ba
domin kotun bata da hurumi a kanta.

Kotun ta kuma ce za ta tsaya iya haka har sai kotun ɗaukakar da gwamnatin jihar Kano ta shigar ta gama nata, duk kuwa da a baya Alƙali Liman ya ce ba zai dakata ba tunda bai samu umarni daga kotun ɗaukaka ƙarar ba.

A yayin zaman shari’ar dai an girke jami’an tsaro a yankin Gyaɗi-gyaɗi da babbar kotun tarayyar take zaune domin samar da tsaro.

Wakilinmu na Kotu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, mai shari’a Liman ya kuma ayyana cewar umarnin da ya bayar tun da farko na cewar kowa ya tsaya a inda yake yana nan bai janye shi ba.

People are also reading