Home Back

Tinubu ya bada umarnin a buɗe kan iyakokin Najeriya da Nijar

premiumtimesng.com 2024/4/29
DATSE BODA: Direbobin tireloli sun yi cirko-cirko da motocin su cike makil da kaya a iyakan Najeriya da Nijar a Katsina

Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin ɗage dukkan takunkumin da Najeriya ta ƙaƙaba wa Nijar, ciki har da bada umarnin buɗe kan iyakokin ƙasashen biyu.

An ƙaƙaba takunkumin tun cikin watan Agusta bayan sojoji ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tchiani sun hamɓaras da gwamnatin Mohammed Bazoum.

Tinubu ya bada umarnin a ranar Laraba, bayan da shugabannin ECOWAS suka cire takunkumi kan Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea, ƙasashen Afrika ta Yamma uku da aka hamɓarar da mulkin dimokraɗiyya baya-bayan nan.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaba Tinubu “ya bada umarnin kan iyakokin Najeriya da Nijar ta ƙasa da ta sama, kuma an cire dukkan takunkumin da aka ƙaƙaba wa ƙasar cikin gaggawa.”

Dukkan kadarorin Nijar da ECOWAS ta riƙe a Manyan Bankunan ECOWAS, su ma an cire masu takunkumi.

 
People are also reading