Home Back

Yadda wata Amarya ta kusa yanke wa Angonta gabansa da wuka ya na barci a Kaduna

premiumtimesng.com 2024/6/26
Knife Man
Knife Man

Wata amarya ai suna Habiba Ibrahim ta kusa guntile gaban mijinta mai suna Salisu Idris yayin da yake barci.

Daily Post ta buga cewa wannan abun tashin hankali ya auku ne ranar 26 ga Mayu garin Kudan.

Salisu mai shekara 40, mazaunin Kudan dake karamar hukumar Kudan a jihar Kaduna na aikin acaba ne Kuma ya auri Habiba watanni hudu da suka gabata.

Ya ce a wannan rana bayan ya dawo sallar asuba ya koma ya kwantar sai Habiba ta hau ruwan cikinsa da wuka ta zuge masa mazagin wando ta jawo lkalaminsa za ta guntile.

Da nan sai ya kwantsama ihu sai makwabta suka shigo cikin gaggawa suka ceceshi, amma ta fara dadara wuƙa akan azzakarin.

“Haka kawai Habiba ta aikata haka domin auren soyayya muka yi kuma tun bayan auren mu ke zaune lafiya. Ban san abinda ya faru ba ta nemi ta guntile min gaba.

An yi gaggawar kai Salisu asibitin Kudan inda daga nan aka kai shi babban asibitin Makarfi inda a yanzu haka yana asibitin A.B.U Shika- Zaria.

Mahaifiyar Salisu, Rabi Salisu ta ce lamarin ya bata mamaki domin tun bayan da aka daura musu aure danta da matarsa ke zaman lafiya.

“Iyayen Habiba sun nemi a sassanta ma’auratan a gida sannan kuma za su biya kudin asibitin laifin da ƴarsu ta aikata.

Habiba dai na tsare hannun ƴan snda sai dai basu ce komai ba akai har yanzu.

People are also reading