Home Back

ANC ta samu kashi 43.5 na sakamakon farko Afirka ta Kudu

dw.com 2024/7/2
Hoto: Zinyange Auntony/AFP

Sakamakon farko na zaben kasar Afirka ta Kudu a wannan Alhamis, ya nuna cewa jam'iyya mai mulki ta ANC ta samu kashi 43.5 cikin 100, bayan kirga kashi 20.2 cikin 100 na kuri'un da aka kada jiya Laraba.

Hukumar zaben kasar ta ce jam'iyyar Democratic Alliance wato DA ta John Steenhuisen ta samu kashi 24.7 cikin 100 na kuri'un, yayin da Economic Freedom Fighters EFF ta Julius Malema ke da kashi 8.9 cikin 100.

Tuni dai dama masana suka yi hasashen cewa zai yi matukar wuya jam'iyyar ANC mai mulki ta shugaba Cyril Ramaphosa ta samu rinjyen kuri'un da za su bata damar ci gaba jan ragamar mulkin kasar, har sai ta yi hadin gambiza da kananan jam'iyyun adawa.

People are also reading