Home Back

Zan mai da hankali kan inganta tsaro a jihar Bauchi– Bala

bbc.com 2024/8/25
Sanata Bala Muhammad

Asalin hoton, OTHERS

Gwamnan jihar Bauchi a arewacin Najeriya Sanata Bala Muhammad ya shaida wa BBC cewa lambar yabon da wata gidauniya da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya suka karramashi da ita, babbar nasara ce.

Sanata Bala ya ce an ba shi lambar yabo ta ayyukan birane, sakamakon irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi a jihar Bauchi, ya kuma ce a yanzu zai mayar da hankali kan kara inganta tsaro a jiharsa.

''Tsaro na daya daga cikin abin da zai kawo hubbasa wajen cigaban garuruwa da biranen da kauyukanmu, idan kauyuka ba su zauna lafiya ba, to kuwa birane ba za su zauna lafiya ba. Ya zama dole mu matsa domin ganin ana zuwa gona da makaranta, kuma kowa yana aiki, jami'an tsaro ana ba su tallafi, da jami'an sa-kai,'' in ji Gwamna Bala.

Sanata Bala ya kuma tabo batun bai wa malamai da sarakunan jiharsa girma da kimarsu: ''Za a gyara albashin sarakuna da limamai ta yadda su ma za su kula da na su iyalan.''

A baya dai lokacin da aka yi taro na gwamnonin arewacin Najeriya, gwamnonin yankin sun yi korafin cewa an mayar da yankinsu saniyar-ware, kuma Sanata Bala ya kara jaddada cewa yankin arewa maso gabas na cikin wani yanayi da koma-baya ta kowanne fanni.

''Kamata ya yi a ce duk ayyukan cigaba mu ma ana sanya mu a ciki, misali kan batun hanyar jirgin kasa, yankin arewacin Najeriya ne na farko da ya fara samu a wancan lokacin, amma a yanzu an manta da mu tun ma gwamnatin baya da ta wuce.

Idan har ba mu samu hanyar jirgin kasa ba, to babu ta yadda za a dauki kayan abinci da ma'adinai da muke da su wanda kowa ya san yankin arewa maso gabas da arewa ta tsakiyar Najeriya na da tarin ma'adinai, amma sai ya kasance idan ka tashi za ka je jihar Filato babu hanyar da za ka je cikin sauki,'' in ji Sanata Bala.

Wasu dai na mamakin yadda mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya fito daga arewa maso gabashin kasar, amma kuma yankin na koma-baya.

A kan haka gwamnan ya ce ba lallai mataimakin shugaban kasa ya iya wannan yakin inganta yankin arewacin kasar shi kadai ba, watakil ma wani ministan gwamnati zai fi shi samun dama.

Kan batun bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu da harkokin kudu da shugabanci da ake ganin gwamnoni kamar ba sa son hakan, gwamnan Bauchin ya ce gwamnatin tarayya ke musu barazana.

Ya ce a yadda ake tafiya suna bakin kokarinsu, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya kawo hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihohi da kananan hukumomi wato ta hanyar asusun hadin gwiwa.

A karshe Sanata Bala ya yi kira ga gwamnatin tarayya, da cewa: ''A gaskiya ya kamata a ji tausayinmu, a tuna muna da dimbin al'umam.''

People are also reading