Home Back

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro a Wani Kwanton Bauna a Jihar Zamfara

legit.ng 2024/5/20

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi wa jami’an rundunar tsaron jihar Zamfara (CPG) waɗanda aka fi sani da Askarawan Zamfara kwanton ɓauna.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'an rundunar mutum uku bayan sun yi musu wanton ɓauna a unguwar Jambako da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar.

'Yan bindiga sun hallaka Askarawan Zamfara
'Yan bindiga sun yi wa Askarawan Zamfara kwanton bauna Hoto: @daudalawal Asali: UGC

Wani majiya mai suna Sanusi Muhammad ya shaida wa wakilin jaridar Leadership cewa ƴan bindigan sun yi wa jami’an na CPG kwanton ɓauna a Tungar Nayarciga kan hanyarsu ta zuwa garin Faru.

A cewarsa, ƴan bindigan sun kuma kwashe makamansu da baburansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin ya haifar da tashin hankali da fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Asali: Legit.ng

People are also reading