Home Back

Aiki Ja: Gwamna Ya Sallami Ma'aikata 10,000 da Mai Gidansa Ya Ɗauka, Ya Zargi Badaƙala

legit.ng 2024/7/5
  • Rigimar siyasar jihar Rivers ta sake sauya salo tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da kuma mai gidansa, Nyesom Wike
  • Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Wike ya yi a karshen mulkinsa inda ya zargi rashin bin tsari a daukar ma'aikatan
  • Gwamnan ya sha alwashin daukar sabbin ma'aikata tare da bin duka tsarin da ya dace ba tare da nuna wariya ko fifiko ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Yayin da rikicin siyasar jihar Rivers ke kara ƙamari, Gwamna Siminalayi Fubara ya ballo liki.

Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya yi a lokacin mulkinsa.

Gwamnan ya ce bai amince da yadda aka bi tsarin daukar aikin ba inda ya ce akwai kura-kurai a ciki, Punch ta tattaro.

Wike ya dauki dubban matasa aiki a ma'aikatun jihar domin cike gurbin wadanda suka bari da kuma inganta harkokin gwamnati.

Bayan soke daukar aikin, Fubara ya yi alkawarin daukar wasu ma'aikata cikin tsari ba tare da nuna fifiko ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, gwamnan ya nuna damuwa kan yadda aka shigar da wasu daga ƙananan hukumomi 23 saboda siyasa ba tare da bin tsari ba.

"Lokacin da muka zo mun samu badakala na daukar ma'aikata 10,000 a kananan hukumomi 23."
"An yi bincike kan wadanda aka dauka aikin inda muka gano 60% sun zarta shekarun da ake bukata."
"Mafi yawansu an saka sunayensu ne saboda kawai sun san wasu ƴan siyasa da suka kawo sunayensu."

- Sim Fubara

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading