Home Back

Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Na Zanga-zanga Kan Ƙarin Ƙudin Wutar Lantarki A Nijeriya

leadership.ng 2024/6/26
Ƙungiyar Ƙwadago Ta NLC Na Zanga-zanga Kan Ƙarin Ƙudin Wutar Lantarki A Nijeriya

Ɗaruruwan jami’an ƙungiyar ƙwadago a Nijeriya suka yi dafifi a fadin ƙasar domin nuna rashin amincewarsu ga ƙarin ƙudin wuta da gwamnati ta yi a watan da ya gabata.

BBC Hausa ta rawaito cewa, Gwamnatin dai ta yi ƙarin ne saboda cire tallafin lantarki da ta yi, inda ƙarin ya shafi masu samun wuta ta tsawon awanni 20 ko fiye da haka da ake kira “Band A”, inda aka ƙara musu naira 172 da farko.

To sai dai daga bisani gwamnati ta rage yawan kuɗin da naira 19, inda yanzu haka suke biyan naira 206 a kan kowane “unit)

Ba wannan ne karon farko ba da ƙungiyar ƙwadago ke ɗaukar matakin zanga-zanga ba amma kuma ba kasafai jama’a ke ganin tasirin matakn nasu ba.

Abin tambaya yanzu shi ne ko wannan matakin zanga-zangar kan wutar lantarki zai sa gwamnati ta sauka daga kan bakanta?

People are also reading