Home Back

Manyan Dabarun Kiwon Zuma A Nijeriya

leadership.ng 2024/5/16
Manyan Dabarun Kiwon Zuma A Nijeriya

Ko shakka babu, fannin kiwon Zuma a Nijeriya na da matukar tsawon tarihi, musamman wajen hawa da sauka da kuma fannin tattalin arziki ga masu wannan sana’a a fadin kasar nan.

Kiwon Zuma ba sabon abu ba ne a tsakanin al’ummar Afirka, domin kuwa an shafe shekara da shekaru ana yi, musamman a yankunan Sahel.

Har ila yau, kasancewar ganin ana samun karancin Katako da Timba a yankunan na Sahel, ya sa masu yin wannan kiwo fara amfani da Tukwane da kuma Ciyawa, don yin kiwon zuma wanda wasu ke ganin wadannan a matsayin kayan gargajiya, wadanda kuma suka fi dacewa da wannan kiwo a Nijeriya.

Wasu daga cikin masu wannan kiwo na zuma, sun fi son gina gidan zumar  a kasa, domin kuwa a nasu ganin da kuma ilimin; wadanan gidaje sun fi jima, don kuwa suna kai wa har zuwa karshen shekara ba tare da an sauya musu wani gidan daban ba.

Wannan dabarar kiwon zuma a gargajiyance, na daya daga cikin dabarun da ake amfani da ita a Nijeriya. Nau’i na farko da ake amfani da shi wajen wannan kiwo na zuma shi ne, amfani da Tukunya; sai kuma nau’i na biyu da ake ginawa a kan Tukunya. Dukkannin wadanannan nau’ika biyu, ana dora su ne a tsakanin Gwafar bishiya.

Amfani Da Tukunyar Laka A Matsayin Gidan Kiwon Zuma:

Wannan hanya kusan ta fi sauki, sannan kuma ita ce hanya mafi sauki tare da juriya wajen kiwon wannan zuma a gargajiyance.

Dabarun Kiwon Zuma A Zamanance:

Mafi akasarin wannan dabara ta kiwon zuma a zamanance, Lorenzo Lorraine Langstroth ne ya samar da ita.

Har ila yau, wannan hanya na da matukar sauki; domin kuwa akasari bayan zuma ta kammala gina gidanta, sukan tashi su kuma shiga wani dakin zuman daban.

Haka zalika, mafi yawan sauran gidajen zuma na zamani da ake gani a yau, dabaru ne da aka samu daga wurin Langstroth; wanda kuma ake yi masa lakabi da jagoran ginin gidan kiwon zuma na zamani.

Wannan hanya ta zamani, na  daya daga cikin wadda ake amfani da ita a Nijeriya, wajen kiwon zuma.

Kazalika, a wannanbangare; zumar ce da kanta ke gina dakin nata na kwana, amma inda matsalar take kadar shi ne na rashin samar wa da dakin wata kariya, domin kuwa zai iya karyewa a cikin sauki.

Sai dai, masu sarrafa irin wannan daki na kiwon zuma; na bukatar amfani da injinan da ke aiki da wutar lantarki, wanda hakan zai bai wa zumar damar zuba tukarta a cikin sauki ba tare da wata matsala ba.

Har ila yau, akwai kuma irin wannan dabarar; wadda Farfesa G.F. Townsend na jami’ar Guelph  da ke Kasar Kanada ya kirkiro da ita.

Mafi akasarin lokuta, an fi amfani da wannan dabara; wajen zuba zuma mai fada wadda aka fi samu a yankunan Afirka.

An kuma fi bai wa wanda zai fara wannan kiwo na zuma shawarar yin amfani da wannan dabara, domin kusan ta fi sauki.

People are also reading