Home Back

Kotu Ta Yi Magana Yayin da Ake Jiran Yanke Hukunci Kan Sahihancin Tube Sarkin Kano

legit.ng 2024/7/6

Jihar Kano - Rahotanni daga jihar Kano sun nun cewa za a ɗan samu jinkirin yanke hukunci kan sahihancin dokar masarautar Kano 2024 da ta tube sarakuna biyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Yayin da mutane ke dakon jin wane hukunci babbar kotun tarayya za ta yanke, an ɗage karanto hukuncin zuwa ƙarfe 2:00na rana yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024.

Muhammadu Sanusi da Aminu Bayero.
Kotu ta dage yanke hukunci a shari'ar masarautar Kano zuwa karfe 2:00 na rana Hoto: Masarautar Kano Asali: Twitter

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, sabuwar dokar da majalisar dokokin Kano ta amince da ita a watan Mayu, ta jawo rigima bayan Gwamna Abba Kabir ya rattaɓa hannu.

Sabuwar dokar ta kai ga tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, tare da rusa sababbin masarautu hudu da Ganduje ya kirkiro da suka hada da Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Har ila yau dokar ta kuma mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar sarauta a matsayin Sarki na 16.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Aminu Babba Danagundi, Sarkin Dawaki Babba, ya kalubalanci halaccin wannan sabuwar doka a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Kano.

Danagundi ta hannun lauyansa, Chikaosolu Ojukwu (SAN), ya roki kotu da ta soke dokar, ma'ana ta tabbatar da Aminu Ado Bayero a matsayin halastaccen Sarkin Kano.

Bayan sauraron ƙorafin ranar Juma’ar da ta gabata, Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman na babbar kotun ya dage shari’ar zuwa yau Alhamis.

A halin yanzu an dage zaman kotun da safiyar Alhamis din nan zuwa karfe 2:00 na rana kamar yadda magatakardan kotun ya sanar.

Asali: Legit.ng

People are also reading