Home Back

Garkuwa Da ‘Yan Makaranta: Nijeriya Ba Za Ta Sake Biyan Kuɗin Fansa Ba – Tinubu

leadership.ng 2024/5/8
Gwamnati Ta Dakatar Da Daraktocin Hukumar Sufurin Jiragen Sama 5 Sa’o’i Kadan Bayan Sauke Shugabanninsu

Yau shekaru goma cur tun da aka sace ‘yan mata 276 cikin dare daga makarantar su da ke garin Chibok a yankin arewa-maso-gabashin Nijeriya. Harin na Boko Haram ya girgiza duniya. Daga London har zuwa Washington, masu zanga-zanga sun riƙa ɗaga kwalayen da aka rubuta #BringBackOurGirls — maudu’in da iyalan ‘yan matan suka wallafa don matsa wa gwamnatin su da ba ta ɗauki wani mataki ba don ta yi wani abu. An ɗauki kusan mako uku kafin Shugaban Ƙasar Nijeriya na wancan lokaci, Goodluck Jonathan, ya ma fitar da sanarwa. 

A cikin watan Maris ɗin nan da ya gabata, an sace yara 137 daga wata makaranta da ke Jihar Kaduna a arewa-maso-yammacin Nijeriya, sai aka tuno da abin da ya faru a Chibok. Tambayar da ‘yan Nijeriya da sauran jama’ar duniya ke yi ita ce, shin me ya sa bayan an shafe shekaru goma har yanzu irin wannan ta’asar take faruwa?

A wannan karon, ba kamar Chibok ba, bayan sati biyu aka dawo da ‘yan makarantar, don an baza jami’an tsaro da na leƙen asiri domin ceto su. Sai dai duk da haka, ana ci gaba da nuna damuwa kan satar mutane da ake yi a ƙasar da ke da mafi yawan al’umma a Afirka. Nasarar da aka samu a Jihar Kaduna ta kawo wa iyalai sauƙi da kuma yabo ga sojoji, amma duk da haka gwamnati ba ta da wani tunani na yaudarar kai – dole ne a kawar da matsalar garkuwa da mutane gaba ɗaya.

Hanyar da za a fara bi ita ce, a fahimci yanayin yadda barazanar ke sauya kamanni. Kalmar Boko Haram dai na nufin “Ilimin Boko haramun ne” kuma tana nuna ƙarfin aƙidar masu tada ƙayar baya da ke da’awar jihadi suke adawa da ainihin manufar Nijeriya. A yau, ‘yan ƙungiyar Boko Haram dai sun tarwatse, kuma sace-sacen jama’a da ake yi duk aikin ƙungiyoyin masu aikata laifi ne. Babu wata aƙida a nan: sace mutane ya zama haramtacciyar masana’anta inda ake biyan kuɗin fansa. A cikin kwanaki kaɗan da kai hari a Jihar Kaduna, masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya kuɗin fansa har naira biliyan 1 (wato dala 600,000).

Ba a biya ko sisi ba. A matsayi na na Shugaban Ƙasa, na bayyana ƙarara cewa, tilas a daina biyan kuɗin fansa. Yanke shawarar a riƙa biyan kuɗin fansa yana dauwamar da matsalar ne kawai. Dole ne a kawar da wannan gungun masu cutar jama’a. A halin yanzu, dole ne a tsananta hukunta masu laifi: a daina biyan su ko kwabo, kuma a ɗau matakan tsaro a kan su.

Amma matse kasuwar satar mutane don neman kuɗin fansa zai haifar jawo wasu mutanen zuwa cikin ta. Idan har za mu guji tura mutanen zuwa cikin wasu laifuffukan da ke sa ’yan Nijeriya na yau da kullum su ji babu tsaro, to dole ne mu magance abubuwan da ke ingiza su ciki: su ne talauci, rashin daidaito, da ƙarancin damarmaki. Ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka za su iya samun sauƙin samun masu taya su ta’asa daga cikin masu zaman kashe wando, ko kuma masu tsammanin samun wani aiki.

Kusan kashi 63 cikin ɗari na ‘yan Nijeriya matalauta ne ta fuskoki daban-daban. Suna fama da matsalolin tattalin arziki sakamakon gazawar gwamnatocin da suka shuɗe wajen magance matsalar tattalin arzikin Nijeriya. Cikas na tsare-tsaren kuɗi da kasafin kuɗi sun hana cigaban ƙasar, lokacin da ƙarin yawan al’umma ke buƙatar haɓakar tattalin arziki don su ci gaba da ingantacciyar rayuwa.

Biyan tallafin man fetur da aka yi shekaru da yawa ana yi ya riƙa ƙarar da kuɗaɗen jama’a ne. Ya zuwa shekarar 2022, kuɗin ya kai dala biliyan 10—fiye da dukkan kuɗaɗen da gwamnati ta kashe kan ilimi, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa a cikin kasafin dala biliyan 40. Iyakance kuɗaɗen da ke yawo don tallafa wa darajar naira ta kawo cikas ga zuba jari kuma ta haifar da ƙarancin kuɗaɗen waje. Mun shafe shekaru da yawa muna fansar kan mu da kuɗi. Lokacin da gwamnati ta ta karɓi ragamar mulki a watan Mayu da ya gabata, mun fuskanci tarin basussuka.

Kamar yadda muke yi da masu garkuwa da mutane, dole ne mu yi da gaske da tattalin arziki. Dole ne a kawar da sauye-sauyen kasuwanci marasa alfanu. Kamar yadda aka yi zato, kange darajar naira ne ya sa ta faɗo. Ganin cewa Nijeriya ƙasa ce mai shigo da abinci, farashin matsakaicin ƙunshin cefane ya yi tashin gwauro zabo. Cire tallafin man fetur, a ƙasar da yawancin kamfanoni da gidaje suka dogara da janareta don samar da wutar lantarki, shi ma ya yi tasiri sosai. Waɗannan sauye-sauyen sun haifar da ƙuncin rayuwa a faɗin Nijeriya; har yanzu ana jin raɗaɗin su. Amma duk da haka babu wata hanyar da ta fi dacewa: waɗannan da sauran sauye-sauye masu wahala sun zama dole a yi su domin magance lalacewar tattalin arzikin da ke faruwa a daidai lokacin da ake fama da rashin tsaro.

Ana iya ganin alamomin farfaɗowar tattalin arziki a yanzu. A cikin watanni huɗu na farkon wannan shekarar, shigowar kuɗaɗen ƙasashen waje ya kusa yin daidai da na gaba ɗayan shekarar da ta gabata. An kawar da biliyoyi na tarin musayar kuɗaɗen waje a babban bankin ƙasar, lamarin da ya bai wa masu zuba jari daga ƙasashen waje ƙwarin gwiwar su zuba jari a cikin mafi girman tattalin arziki a Afirka, don sun san cewa za su iya fita da ribar da suka samu. Naira ta fara daidaituwa ne bayan faɗuwar ta ta farko kuma har ta samu gagarumar nasara a kan dala.

Maganar cikakken tattalin arziki na iya zama abu mai kamar wuya idan an yi la’akari da ƙalubalen rashin tsaro. Amma idan ba tare da an samar da ginshiƙai ba, ba zai yiwu a samu damar samar da yanayin da kamfanoni masu zaman kan su za su bunƙasa ba, a samar da ayyukan yi, a kuma samar da damar da za a ba su a cikin ƙasar. Ta haka ne za mu tabbatar da cewa yara za su iya zuwa makaranta ba tare da wata fargaba ba.

Ga duk wanda ke shakkar alƙiblar da muka fuskanta, ya kamata a yanzu ya fahimta. Ba za a ƙara biyan kuɗin fansa ba—ba ga masu garkuwa da mutane kaɗai ba, ba kuma ga waɗannan tsare-tsaren da suka riƙe wuyan mutanen mu ta fuskar tattalin arziki. Za a ‘yantar da ‘yan Nijeriya, tare da tattalin arzikin su.

People are also reading