Home Back

Sanatan PDP Ya Koka Kan Kara Kudin Wutar Lantarki, Ya Ce Yana Kashe N1m a Kowane Wata

legit.ng 2024/5/17
  • A yayin da gwamnati ta dage kan cewa akwai alfanu a kara kudin wutar lantarki, wani sanatan PDP ya ce koka kan tsadar wutar
  • Sanata Olubiyi Fadeyi, ya ce yana kashe Naira miliyan biyu wajen biyan kudin wutar lantarki da kuma sayen man dizal a kowane wata
  • Fadeyi ya yi nuni da cewa da ana samun wutar lantarkin yadda ya kamata, da bai kashe wadannan kudin wajen sayen mai ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sanatan Osun ta tsakiya, Olubiyi Fadeyi, ya ce yana kashe zunzurutun kudi har Naira miliyan daya-daya wajen biyan kudin wutar lantarki da kuma sayen man dizal a kowane wata.

Fadeyi ya bayyana haka ne a wajen zaman bincike kan ‘bukatar dakatar da karin kudin wutar lantarkin da ake son yi’’ a ranar Litinin a Abuja, rahoton jaridar The Punch.

Sanatan PDP ya koka kan kara kudin wutar lantarki ga kwastomomin Band A
Sanata Olubiyi Fadeyi ya ce yana kashe N1m a biyan kudin wutar lantarki kowane wata. Hoto: @ajagunnla1 Asali: Twitter

Sanatan ya koka kan cewa mayar da kwastomomi zuwa Band A bai dace ba saboda ba sa samun isasshiyar wutar lantarki da ta kai darajar kudin da suke biya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta kara kudin lantarki

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Najeriya ta amince da karin kudin wutar lantarki da kaso 340 ga kwastomomin da ke karkashin Band A.

Channels TV ya rahoto mataimakin shugaban hukumar NERC, Musliu Oseni, ya ce kwastomomin da ke karkashin Band A za su fara biyan N225/KwH daga N66 da aka saba biya.

Tun da farko, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce ‘yan Najeriya da aka dora kan Band A a yanzu suna kashe kudi kadan wajen sayen dizal da man fetur.

Karin kudin lantarki: Sanata Fadeyi ya koka

Amma Fadeyi, a martanin da ya mayar, ya ce:

“Ina kashe Naira miliyan daya akan wutan lantarki, sannan ina kashe wata Naira miliyan daya akan dizal, wannan ban da kudin da nake kashewa a sana’o’in da nake yi.
"Idan da ana samun wutar lantarkin yadda ya kamata, to da ba zan kashe wadannan makudan kudin wajen saka mai a janareta na ba."

Fadeyi ya kara da cewa, ya kamata hukumar NERC ta kara himma wajen aiwatar da ayyukan da doka ta dora ta akai domin batun samar da lantarki ya tafi yadda ya kamata.

Gwamnati za ta cefanar da DisCos

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kammala shiri na sayar da wasu daga cikin kamfanonin rarrabawa jihohi wutar lantarki (DisCos).

Yayin da wutar ta gaza daidaituwa, gwamnatin tarayya ta ce bankuna da kamfanin AMCON ba su da karfin fasahar tafiyar da kamfanonin rarraba wutar lantarkin.

Asali: Legit.ng

People are also reading