Home Back

Hotunan dabbobin layya a kasuwar Dei-dei da ke Abuja

bbc.com 2024/7/5
Rago a kasuwar dabbobi da ke Abuja

Yayin da babbar sallah ke ƙara ƙaratowa, farashin dabbobi ya yi tashin gwauron zaɓi a kasuwannin Najeriya da makwabtan ƙasashe.

Raguna a kasuwar Dei-dei
Bayanan hoto, A kasuwar Dei-Dei da ke Abuja, dillalai sun shaida wa BBC cewa farashin rago a wannan shekara ya fara daga naira 80,000 zuwa miliyan ɗaya.
Rago
Bayanan hoto, Ya danganta da irin kiwon da rago ya samu.
Raguna
Bayanan hoto, Masu sayar da ragunan sun alaƙanta hakan da tsadar sufuri da kuma kuɗin abincin dabbobin.
Shanu
Bayanan hoto, Bayanai sun nuna cewa farashin shanu a kasuwannin Abuja ya fara ne daga naira 500,000 zuwa naira miliyan 3.5.
Shanu
Bayanan hoto, Masu wadata kan sayi shanu domin yankawa a ranar sallah
People are also reading