Home Back

Abin Murna: Gwamnan Jigawa Ya Mayar Da Wankin Ƙoda Kyauta A Jihar

leadership.ng 3 days ago
Abin Murna: Gwamnan Jigawa Ya Mayar Da Wankin Ƙoda Kyauta A Jihar

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da samar da magunguna kyauta da suka haɗa da wankin ƙoda ga masu ciwon ƙoda a cibiyoyin lafiya biyar dake jihar.

Wannan shiri, na ɗaya daga cikin ƙudirori 12 na Gwamna Umar Namadi, da nufin tabbatar da samar da lafiya ga ɗaukacin mazauna yankin, ba tare da la’akari da matsayin tattalin arzikinsu ba.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abdullahi Kainuwa ya bayyana cewa za’a samar da cibiyoyin wankin ƙodar a manyan asibitocin Dutse da Ringim, tare da sanya na’urorin gyaran jiki na zamani a manyan asibitocin Hadejia, Kazaure, da Gumel.

Dr. Kainuwa ya jaddada ƙudirin Gwamna Namadi na ganin an samu sauƙin harkokin kiwon lafiya, tare da tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon rashin kudin magani.

Majalisar zartarwar jihar ta kuma amince da kashe Naira biliyan ₦1.5b don gyara da inganta cibiyoyin lafiya 32 a mazabu 30.

Wannan shiri ya haɗa da shigar marasa talakawa 500 daga gundumomin siyasa 287 na jihar zuwa shirin inshorar lafiya kyauta.

Bugu da ƙari, don inganta kiwon lafiya, gwamnatin Jigawa ta ɗauki ma’aikatan kiwon lafiya 1,100, gami da likitoci 200, masu ilimin magunguna, da ma’aikatan jinya.

People are also reading