Kotu Ta Kora Babban Jami'in Kamfanin Binance Zuwa Gidan Gyaran Hali
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare babban jami’in Binance, Tigran Gambaryan, a gidan gyaran hali na Kuje.
Kotun ta umurci a tsare Gambaryan ne har zuwa lokacin da za ta yi hukunci kan belin da ya nema, cewar rahoton jaridar The Punch.
Alƙalin kotun, mai shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ne bayan Gambaryan ya ƙi amsa laifin safarar kuɗaɗe da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ya yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ke yi masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC na zargin kamfanin Binance, Gambaryan, da Nadeem Anjarwalla wanda ya arce kan ɓoye hanyar da suka samu $35,400, 000 a matsayin kuɗin shiga a Najeriya.
Lauyan masu shigar da ƙara ya buƙaci a sanya ranar da za a fara shari'ar. Sai dai lauyan Gambaryan ya roƙi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa.
Daga bisani alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Afrilu domin yanke hukunci kan belin da ya nema da kuma ranar 2 ga watan Mayun 2024, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'in kamfanin Binance da ke tsare a Najeriya ya maka mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da hukumar EFCC a gaban kotu.
Tigran Gambaryan ya shigar da ƙarar ne bisa abin da ya kira tauye masa haƙƙinsa da aka yi kan ci gaba da tsare shi da ake yi.
Asali: Legit.ng