Home Back

'Yan Bindiga Sun Farmaki Ƴan Majalisa 6, Sun Buɗe Masu Wuta a Arewacin Najeriya

legit.ng 2024/7/1

Jihat Benue - Wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki tawagar mambobi biya% na majalisar dokokin jihar Benuwai a kan titin Makurɗi zuwa Gboko.

Shaidan gani da ido ya bayyana cewa ƴan bindigar sun kai wa ƴan majalisar hari a misalin ƙarfe 10:00 a dare a daidai kauyen Tyomu mai nisan kilomita 16 zuwa Makurɗi.

Gwamna Alia na jihar Benue.
Yan bindiga sun buɗe wa motocin ƴan majalisa 6 wuta a Benue Hoto: Fr. Hycinth Iormem Alia Asali: Facebook

A cewar waɗanda suka shaida lamarin, maharan sun fara kai farmak< kan mazauna ƙauyen kafin daga bisani suka koma kan matafiyan da ke wucewa a titin.

Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da harin da rutsa da su, Saater Tiseer, shugaban masu rinjaye a majalisar Benuwai ya tabbatar da lamarin ga wakilin Daily Trust.

Ya ce sun faɗa tarkon maharan ne yayin da suke kan hanyar dawowa daga wurin wani aiki a Gboko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honorabul Tiseer ya bayyana cewa bisa sa'a sun tsira daga mummunan harin ƴan bindigar lami lafiya, babu waɓda ƴa samu ko kwarzane.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar Benuwai, Elias Audu, ya ce an kai wa ƴan majalisar hari da ƙarfe 10:00 a hanyarsu ta dawowa daga ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Ya ce sun je yankin ne domin jin ra'ayoyin jama'a game da kudirin kafa rundunar ƴan sa'kai ta jiha wanda za ta kare rayukan fararen hula.

Audu ya bayyana cewa maharan da yawansu ya haura 40 a kan babura sun yi wa ‘yan majalisar kwanton bauna a Tyo-mu inda suka budewa motocin su wuta.

Ya jero ‘yan majalisar da abin ya shafa da su hada da, shugaban masu rinjaye, Saater Tiseer, mai tsawatarwa, Ipusu Bemdoo, mamba mai wakiltar Logo, Samuel Jiji, takwaransa na mazabar Mata, Simon Gabo da Cephas Dyaku.

Asali: Legit.ng

People are also reading