Home Back

TAIMAKA WA ƳAN TA’ADDA DA KUƊAƊE: Gwamnati ta bayyana sunayen mutum 19, ciki akwai Tukur Mamu, Fatima Isha

premiumtimesng.com 2024/4/30
‘Da gangar aka bari ƴan bindiga suka kai harin gidan yarin Kuje, saboda na yi ta faɗin hakan zai auku – Mamu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sunayen mutum 19 da ta ce sun taka rawa wajen taimaka wa ‘yan ta’adda da kuɗaɗe, ciki har da wasu ‘yan canji shida. Haka dai wani daftarin da aka fitar ya nuna, kuma daftarin ya faro hannun PREMIUM TIMES.

A cikin daftarin, an bayyana sunayen waɗanda aka samu da laifin, kuma Kwamitin Ladaftarwa wanda ke ƙarƙashin jagorancin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a.

Waɗanda sunayen su ya fito a cikin daftarin dai su ne: Tukur Mamu, mawallafin jaridar Desert Herald, kuma mazaunin Kaduna, wanda ke tsare tun cikin 2022 a hannun jami’an tsaro.

Akwai Abdulsamad Ohida, Mohammed Abdurahaman (FNU), Fatima Ishaq, Yusuf Ghazali, Mohammed Sani, Abubakar Muhammad, Sallamudeen Hassan, Adamu Ishak, Hassana Isah, Abdulkareem Musa da kuma Umar Abdullahi.

Kamfanoni Shida Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Kuɗaɗe:

Akwai West and East Africa General Trading Co. Ltd, Setting Bureau De Change Ltd, G. Side General Enterprises, Desert Exchange Ventures Limited, Eagle Square Genaral Trading Co. Ltd, sai Alfa Exchange BDC.

Kwamiti ya bayar da taƙaitaccen bayani kan Wasu da aka samu dumu-dumu da aikata laifin, kuma aka bayyana irin yadda suka taka rawa wajen tura wa ‘yan ta’adda kuɗaɗe.

Tukur Mamu, wanda mawallafin jaridar Desert Herald ne a Kaduna, kuma Kakakin Sheikh Gumi, wanda da shi aka riƙa shiga daji lokacin da Gumi na so mahara su ajiye makamai ita kuma gwamnati ta zauna da su.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda aka kama shi a filin jirgin saman Cairo da ke Egypt, cikin Satumba, 2022, kan hanyar sa ta tafiya Umrah tare da iyalan sa.

A daidai lokacin SSS a Kaduna sun dira gidan sa a Kaduna da ofishin sa, su ka bincike su kakaf. Har yanzu ya na tsare, ya na fuskantar tuhuma.

Kwamiti ya ce Tukur Mamu ya taka rawa “wajen ɗaukar nauyin ta’addanci ta hanyar karɓar kuɗaɗen fansa daga iyalan waɗanda aka kama a harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, ya na kai wa ‘yan ta’adda kuɗaɗen.

Rahoton kwamitin ya ce Mamu ya kai wa ‘yan ta’adda sama da Dala 200,000, domin su saki waɗanda suka kama.”

Mutun na biyu a sunayen shi ne Ohida, wanda a cikin bayanin kwamiti aka ce babban jami’in ‘yan ta’addar ISWAP ne da ke Okene.”

Shi ake zargi da kai hari a Cocin St. Francis Catholic Church, Owo, Jihar Ondo a ranar 5 ga Yuni, 2022 da kuma Kuje, 5 ga Yuli, 2022.”

Shi kuwa Sani mai shekaru 37, mamba ne na ‘yan ta’addar Ansaru, kamar yadda kwamitin ya tabbatar.

An ce an yi masa tirenin a ƙarƙashin ƙasirgunin ɗan ta’adda, Muktar Belmokhtar (Mai Ido Ɗaya), gogarman ɗan Al-Qaeda a Maghreb. An bindige Belmokhtar cikin 2016.

An ce Sani kafinta ne ƙwararre, kuma ya naƙalci tsara wa ‘yan ta’adda lambobin isar da saƙonni na sirri, da kuma ɗana nakiya.

An gano cewa ya na daga cikin waɗanda suka gudu a farmakin da ‘yan ta’adda suka kai Kurkukun Kuje, cikin Yuli, 2022.

Kwamitin ya ce Sani mai tsaron ƙofa ne ga Shugaban ANSARU, Mohammed Usman, wanda aka fi sani da Khalid Al-Bamawi.

Kuma an tabbatar ya yi aikin kai saƙonni da nuna hanya zuwa ga ‘yan ta’addar AQIL Katibat cikin dajin Aljeriya da Mali.”

Shi kuwa Abdurrahaman FNU, kwamanda ne na ISWAP a Okene, Jihar Kogi, kamar yadda kwamitin ya ce ya tabbatar.

ISWAP sun raba hanya da Boko Haram cikin 2016, saboda bambancin saɓanin fahimta a ita kan ta aƙidar ta su.

Shi kuma Ishaq, mazaunin Unguwar Sarki ce a Kaduna. An ce shi ne ke aika wa ISWAP Okene kuɗaɗe.”

Kwamiti ya ce shi ke raba kuɗaɗe ga matan ‘yan ta’addar da aka kashe mazan su da suke zaman takaba.”

Ita kuwa ɗaya matar, Fatima Isah, matar Abdulkareem Musa ce, wato Abu Khalid ko Abu Aiman, inji kwamitin.

“Ta na karɓar kuɗaɗe daga ISWAP sai ta je ta raba wa matan su.”

Mijin ta Musa kuwa babban kwamandan ISWAP ne da ke jihohin tsakiyar Najeriya.

Ya yi aiki a matsayin manajan Star Bread, wanda mallakin ISWAP ne da ake yi a tsallaken Masallacin Abusito, yankin Irubucheba, cikin Jihar Kogi, kafin a kama shi a tsare tun cikin 2021.”

Shi kuwa Ghazali ɗan Kano ne, wanda aka kama da laifin tura wa Surajo Muhammad Naira miliyan 20. Surajo na ɗaya daga cikin ‘yan Najeriya shida da ke ɗaure a Dubai, tun cikin 2020, bisa laifin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.

Hukuncin Da Aka Zartas Kan Su:

Bisa tsarin da Sashe na 54 na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022 ta tanadar, kwamiti ya bada shawara kamar haka:

A ƙwace dukkan dukiyoyi da kadarorin da waɗannan mutane da kamfanoni suka mallaka, ba tare da yin sanarwa ba.

Idan an ƙwace dukiyoyi da kadarorin su, a sanar wa kwamitin hakan ba tare da ɓata lokaci ba.

“Sannan a aika da rahoton su ga NFIU, Hukumar Sa-ido Kan Hada-hadar Kuɗaɗe, domin ci gaba da nazarin harkokin hada-hadar kowanen su.

Sannan kuma a aika da sunayen waɗanda suka yi hada-hadar kuɗaɗe da su.

Kwamitin ya ce wannan hukunci ya shafi dakkan kadarori ko wata dukiyar da kowanen su ya mallaka, ba wai sai wadda aka yi hada-hadar ta’addanci da ita ba. Ko gida ko fili duk a ƙwace.”

Haka duk wata kadarar da kowane ake zargin ya mallaka ta haɗin gwiwa da wani can wanda ba ya mu’amala da ‘yan ta’adda, ita ma a ƙwace ta kawai.

People are also reading