Home Back

Tsohon Daraktan CBN Ya Tona Asirin Emefiele a Kotu Kan Sauya Fasalin Naira

legit.ng 2024/7/6
  • Hukumar EFCC ta gabatar da shaida a gaban babbar kotun Abuja a shari'ar tsohon gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele
  • Tsohon daraktan sashin ayyuka na CBN, Ahmed Umar, ya faɗi yadda Emefiele ya aiwatar da tsarin sauya fasalin Naura ba tare da amincewa ba
  • EFCC dai na zargin tsohon gwamnan da kashe biliyoyin Naira wajen buga sababbin kudi N684.5m kaɗai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A jiya Talata, 28 ga watan Mayu, 2024 aka ci gaba da sauraron shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele.

A wannan zama, tsohon daraktan ayyuka a CBN, Ahmed Umar, ya faɗawa kotu dukkan abin da ya sani game da canjin takardun kuɗi N200, N500 da N1,000.

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Tsohon daraktan CBN ya bayar da shaida kan yadda aka canja fasalin Naira Hoto: Mr. Godwin Emefiele Asali: UGC

Ahmed ya shaidawa kotu cewa Emefiele ya yi gaban kansa ya canja takardun kuɗi a ƙarshen 2022 ba tare da amincewar kwamitin gwamnonin bankin ba, Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta sake gurfanar da Emefiele a gaban mai shari'a Maryanne Anenih ta babbar kotun Abuja ranar 15 ga watan Mayu.

Sai dai a wannan karon EFCC ta maka tsohon gwamnan a kotu ne kan tuhumar canjin Naira da buga sababbin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba.

A tuhume-tuhumen mai lamba CR/264/2024, EFCC ta yi zargin cewa Emefiele ya aiwatar da tsarin sake fasalin Naira ba tare da amincewar majalisar gudanarwa ta CBN da Shugaban Kasa Buhari ba.

Ya ce ba tare da amincewar shugaban ƙasa ba, Emefiele ya kashe N18.96bn wajen buga sababbin takardun kudi na naira miliyan N684.5m.

A zaman baje kolin hujjoji da aka fara ranar Talata, EFCC ta gabatar da tsohon daraktan ayyuka na CBN, Ahmed Umar, a matsayin shaida na farko, The Nation ta ruwaito.

Da yake bayanin yadda aka yi, Ahmed Umar ya shaida wa kotun cewa a shekarar 2022 aka umurci sashen da yake jagoranta ya tsara sabon fasalin kuɗin Najeriya.

"Mun tsara kundin muka miƙa ofishin mataimakin gwamnan CBN mai kula da sashin ayyuka, shi kuma ya miƙa wa gwamna kuma aka sa shi cikin abubuwan da kwamitin gwamnoni zai duba."

Shaidan ya ce an gabatar da kundin sauya fasalin Naira ga kwamitin gwamnonin domin tantancewa a ranar 26 ga Oktoba, 2022, amma kwamitin bai amince da shi ba.

Tsohon daraktan ya shaida wa kotun cewa ya fara aiki a CBN shekaru 35 da suka gabata kuma ya yi ritaya a watan Yulin 2023. A karshe kotu ta karɓi shaidarsa.

EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika

A wani rahoton kuma hukumar yaƙi da cin hamci ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika ne tare da ɗan'uwansa, Ahmad Abubakar Sirika da wani kamfani kan badaƙalar N19.4bn.

Asali: Legit.ng

People are also reading