Home Back

‘Yan Sanda sun damƙe mutum 8 dangane da zargin kisan jami’an su a Jihar Delta

premiumtimesng.com 2024/4/29
Rundunar ƴan sandan Kano ta tsinci gawar wasu ma’aurata biyu kulle a ɗaki a Dawakin Tofa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa ta damƙe mutum 8 da ake zargi da hannu wajen kashe zaratan ‘yan sanda biyar a Jihar Delta.

Tun da farko dai mutum uku aka fara kamawa, amma da ana nutsa cikin kogin bincike, an sake kamo mutum uku.

An ce an kama mutum biyar a wurare daban-daban, kuma su ne suka bayyana inda sauran uku ɗin suke, har aka je aka yi nasarar cafke su.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan, Adejobi, ya ƙara da cewa an sami nasarar kama su ne bayan wani ƙwaƙƙwaran bincike.

Ya ce waɗanda ake zargin su na hannun ‘yan sanda ana yi masu tambayoyi. Kuma ana ci gaba da bincike.

Wannan jarida ta buga labarin yadda ‘yan bindigar Delta sun sake kashe ‘yan sanda 6, wasu 6 an rasa inda suke.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi shelar cewa an kashe zaratan jami’an ta shida, yayin da wasu shida kuma an neme su an rasa, bayan da ‘yan bindiga suka yi masu kwanton-ɓauna a Jihar Delta.

Kakakin Yaɗa Labaran Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, a Abuja, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya buga a shafin tiwita, wato X.

A ranar Asabar ya saki sanarwar, amma bai bayyana ranar da aka kashe ‘yan sandan da kuma ranar da su ma waɗanda aka rasa inda su ke ɗin suka ɓata ba.

Adejobi ya ce ‘yan sandan da kashe da waɗanda ake nema ɗin sun je ne domin binciken yadda wasu abokan aikin su uku suka ɓace a cikin Dajin Ohoro, cikin Jihar Delta.

A can cikin dajin ne ‘yan bindiga suka yi masu kwanton-ɓauna, suka kashe har da insifeto biyu, sajen huɗu, yayin da ake neman insifeto huɗu, sajen biyu har yau shiru, babu labarin su.

Adejobi ya ce ‘yan sandan da aka kashe sun haɗa da Sufeto huɗu, Abe Olubunmi, Friday Irorere, Sajen Kuden Elisha, Sajen Akpan Aniette, Sajen Ayere Paul da Sajen Ejemito Friday.”

Sannan kuma ya bada sunayen waɗanda suka ɓace ɗin kamar haka: “Sufeto Onoja Daniel, Sufeto Onogho Felix, Sufeto Emmanuel Okoroafor, Sifeto Joel Hamidu, Sajen Moses Eduvie da Sajen Cyril Okorie.

Amma tuni an gano gawarwakin waɗanda aka kashe, a wani gagarimin shirin neman su da jami’an tsaro suka yi a cikin dajin.

Adejobi ya ce an kama mutum biyar cikin waɗanda ake zargi da wannan mummunan kisan jami’an tsaron.

Kisan na su ya faru a yankin na Jihar Delta, Jihar da aka kashe sojoji 17 a ranar 14 ga Maris.

 
People are also reading