Home Back

Alhazan Najeriya sun koka kan zaftare musu kudin kuzuri

bbc.com 2024/7/3
Mahajjata

Asalin hoton, NAHCON

Mahajjatan Najeriya reshen birnin tarayya Abuja da yanzu haka ke kasar Saudiyya, sun gudanar da zanga-zanga inda suka nuna damuwa game da ba su dala dari biyu, a maimakon dala dari biyar da hukumar jin dadin alhazzan Najeriyar ta musu alkawarin ba su da farko a matsayin kudaden guzuri.

Mahajjatan sun ce suna zargin akwai lauje cikin nadi game da wannan sauyi.

Alhazan sun ce ba haka suka daddale da gwamnati ba kafin su tashi zuwa kasa mai tsarki.

Daya daga cikin mahajjatan birnin tarayya Abuja da BBC ta tattauna da shi ta waya ya ce korafinsu shi ne alkawarin da aka yi musu tun da farko cewa za a basu dala dari biyar, amma daga bisani aka basu dala dari biyu aka ce musu za a cika idan anje kasa mai tsarki.

Ya ce,"Sun ce mana rashin canjin dala ne ya sa ba a bamu cikakken kudin ba, to amma idan an je kasa mai tsarki za a canja ragowar kudin zuwa Riyal a bamu cikon kuzurinmu."

Mahajjatin ya ce," Da muka isa sai abu ya sauya domin a yanzu sun ce mana dala dari biyu ne cikon kuzurin mu maimakon dala dari uku da za a bamu, to abin da ya tunzura mu ke nan."

Wannan mataki na zaftare kudaden kuzurin mahajjatan ba na birnin tarayya kawai ya shafa ba, har ma da na wasu jihohi.

Wani mahajjati daga jihar Nasarawa ya shaida wa BBC cewa, zaftare kudaden kuzurin ma ta fi shafar mata saboda dan kudin da aka basu su rike kafin a cika musu duk sun yi amfani da su musamman wajen sanya hakorin Makka wanda kuma akalla ya kai dala 100.

" A yanzu mata na cikin kunci saboda duk sun yi hidima da kudinsu, a bangaren maza da dan sauki."in ji shi.

BBC ta tuntubi Muhammad Lawan Aliyu, mai magana da yawun hukumar jin dadin alhazai ta birnin tarayya Abuja, wanda ya ce ba laifinsu bane.

Ya ce," Hukumar alhazai ta Najeriya ta ce zata bayar da kuzurin dala dari biyar ga kowanne mahajjati, kuma a lokacin dala a kan 1,250 ta ke, to amma da muka je karbo kudi a wajen banki abin da aka bamu dala shi a kan naira 1,530 kan kowacce dala."

"Wannan ya janyo dole kudin kuzurin alhazai ya sauya saboda idan aka yi lissafi a kan yadda za a samu za a ga maimakon dala dari biyar da farko yanzu kowanne alhaji zai samu dala 415 ne."

Ya ce hukumar alhazai ta kasa ta fito ta yi bayani a kan wannan matsala tare da alkawarin daukar matakin da ya dace.

A mafi yawancin lokuta dai mahajjatan Najeriya kan yi zargi game da kudaden kuzurinsu da wasu lokuta ake rage yawansu ko kuma a samu wadanda za su damfare su.

People are also reading