Home Back

Za A Kara Bunkasa Hadin Gwiwar Tsaro Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka

leadership.ng 2024/4/28
Za A Kara Bunkasa Hadin Gwiwar Tsaro Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka

Da yammacin yau Alhamis ne aka gudanar da taron manema labarai, a ma’aikatar tsaron kasar Sin, inda kakakin ma’aikatar kanar Zhang Xiaogang, ya ce a shekarun baya bayan nan, alakar harkokin soji tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka na kara zurfafa. Kaza lika sassan biyu, sun gudanar da dandalin zaman lafiya da tsaro, da taron musamman kan hakan, suna kuma ci gaba da yin musaya ta kut da kut a dukkanin matakai.

Zhang, ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun ci moriyar hadin gwiwa a sassa kamar na gina tsarin aikin soji, da horas da dakaru, da tsaron teku, da ayyukan wanzar da zaman lafiya, da bunkasa kiwon lafiya, da ayyukan ceton jin kai da na dakile bala’u.

Jami’in ya ce rundunar sojin Sin za ta ci gaba da daukaka akidun gaskiya,

da cimma sakamako na zahiri, da tabbatar da tafiya tare, da amincewa juna, da aiki tare da sauran rundunonin sojin kasashen Afirka, wajen ingiza aiwatar da muhimman manufofi da jagororin su suka cimma matsaya a kai. Har ila yau, sassan biyu za su karfafa tuntubar juna bisa matsayin koli, da hadin gwiwa na zahiri.

A daya hannun za su kara inganta hadin gwiwa mai ma’ana da karko, da samar da tabbacin aminci na tsaro, ta yadda za a gina al’umma mai makomar bai daya bisa matsayin koli tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da bayar da babbar gudummawa ta wanzar da tsaron yankuna da duniya baki daya, da yayata gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama.

Don gane da aiwatar da tsarin rakiyar jiragen ruwa, da rundunar sojin ruwan Sin ke gudanarwa a tekun Aden da yankunan ruwan Somalia kuwa, Zhang Xiaogang ya ce wannan batu ne wanda ba shi da wata nasaba da halin da ake ciki yanzu haka a yankin. Don haka Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin tsaron kasa da kasa, da tabbatar da kariya a hanyoyin tekunan kasa da kasa, da samar da tsarin sufurin teku abun dogaro, wanda zai ci gaba da rake jiragen ruwan Sin da ma na sauran kasashe. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

 
People are also reading