Home Back

FARGABAR AMBALIYA: Ministan Ruwa da Muhalli ya gargaɗi jihohi 18 su kula da tsaftar muhalli don kauce wa ambaliya

premiumtimesng.com 2024/10/6
Flood in Jigawa
Flood in Jigawa

Ministan Harkokin Ruwa da Tsaftace Muhalli, Joseph Terlumum ya bada shawara tare da gargaɗin jihohi 18 a ƙasar nan cewa su kiyaye da tsaftace muhalli domin kauce wa ambaliya da kuma annobar kwalara.

Ministan ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da ambaliya ke ci gaba da mamaye unguwanni da dama a Jihar Legas da wasu garuruwa. Sai dai ta Jihar Legas ɗin ce ta fi muni sosai.

Ministan ya bayyana jihohin da ka iya fuskantar gagarimar ambaliya cewa sun haɗa da Akwa Ibom, Anambra, Adamawa, Benuwai, Bayelsa da kuma Kuros Riba. Sai jihohin Delta, Edo, Jigawa, Kogi, Kebbi, Kaduna, Neja da Nasarawa.

Sauran jihohin da ministan ya yi wa gargaɗin sun haɗa da Ondo, Ogun, Ribas da Gundumar FCT Abuja.

Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da fuskantar ambaliyar musamman a Legas saboda tsananin ruwan sama, a Abuja ma an fuskanci ambaliya cikin makon da ya gabata a wasu yankuna kamar rukunin gidajen TradeMore da ke Lugbe, Abuja, unguwar da kusan kowace shekara sai ambaliya ya shafe ta.

A Arewa maso Yamma kuwa, matsalar ƙarancin ruwan sama da ake fama da shi, ta kai ko a ranar 4 ga Yuli sai da aka yi Sallar Roƙon Ruwa a Katsina.

Damina ba ta kankama ba a Arewa, kamar irin yadda ta kankama a tsakiyar Najeriya da kudancin ƙasar.

People are also reading