Home Back

Euro 2024: Turkiya za ta kara da Netherlands a kwata fainal

bbc.com 2024/10/5
Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images

Turkiya ta kai zagayen kwata fainal za ta fuskanci Netherlands, bayan da ta doke Austria 2-1 ranar Talata a Euro 2024.

Minti daya da take leda Turkiya ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Merih Demiral, haka suka je hutun rabin lokaci.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Turkiya ta kara na biyu ta hanun Merih Demiral daga baya Austria ta zare daya ta hannun Michael Gregoritsch.

Da wannan sakamakon Turkiya za ta buga daf da na kusa da na karshe da Netherlands ranar Asabar 6 ga watan Yuli.

Ranar Talata Netherlands ta ɗura ƙwallo uku a ragar Romania a fafatawar zagaye na biyu a Euro 2024.

Wasannin quarter final a Euro 2024

Ranar Juma'a 5 ga watan Yuli

  • Sifaniya da Jamus a Stuttgart.
  • Portugal da Faransa a Hamburg.

Ranar Asabar 6 ga watan Yuli

  • Ingila da Switzerland a Dusseldorf.
  • Netherlands da Turkey a Berlin.

Ƴan wasan Austria 11: Pentz, Posch, Danso, Lienhart, Mwene, Seiwald, Sabitzer, Laimer, Baumgartner, Schmid, Arnautovic.

Ƴan ƙwallon Turkiya 11: Gunok, Muldur, Bardakci, Demiral, Bardakci, Ayhan, Yuksek, Yildiz, Yilmaz, Kokcu, Guler,

People are also reading