Home Back

Chelsea za ta dauki Tosin daga Fulham

bbc.com 2024/7/6
Tosin Adarabioyo

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta tattauna da mai tsaron bayan Fulham, Tosin Adarabioyo a cikin makon nan.

Ƙungiyar da ke Stamford Bridge na takarar ɗaukar ɗan wasan da Newcastle da Manchester United ke fatan mallaka.

Ƙwantiragin mai shekara 26, zai kare a bana, yayin da bai amince ya ci gaba da taka leda a Fulham a kakar badi ba, wanda ya taka rawar gani a bana.

An fahimci cewar Adarabioyo na son komawa taka leda a birnin Landan, amma a Chelsea, idan hakan bai samu ba ya koma St James Park.

Tsohon wanda ya fara daga makarantar koyon tamaula a Manchester City, bai amince ya karbi tayin ƙwantiragin da zai zama mafi albashi mai tsoka a Craven Cottage a cikin Afirilu ba.

Yarjejeniyar mai tsaron bayan za ta kare a Fulham a karshen watan Yuni.

Adarabioyo zai maye gurbin matashi, Trevoh Chalobah, mai shekara 24, wanda ake bayar da rahoton cewa Man United na son sayen shi kan fara kakar badi.

United za ta buga Europa League a badi a gasar zakarun Turai, bayan da ta lashe FA Cup da cin Manchester City 2-1 a Wembley.

Ita kuwa Chelsea, wadda ta kare a mataki na shida a teburin Premier League da aka kammala, za ta wakilci Ingila a wasan cike gurbin shiga Europa Conference League a badi.

People are also reading