Home Back

Gwamnatin Kano Ta Bude Makarantun Da Ganduje Ya Rufe

leadership.ng 2024/6/26
Gwamnatin Kano Ta Bude Makarantun Da Ganduje Ya Rufe

Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kakaba wa sashin ilimin dokar ta baci, sannan ya kuma sanar da daukar malamai guda 5,643 aiki karkashin shirin BESDA, wanda bankin duniya ya kirkira domin kara kyautata hanyoyin da yaran da ba sa zuwa makaranta za su samu ilimi tare da kakkabe jahilci tsakanin ‘yan Ni-jeriya.

Da yake jawabi a lokacin taron, Gwamna Abba ya bayyana aniyarsa na rungumar harkokin ilimi da kansa domin jan ragamar Jihar Kano zuwa kyakkyawan matsayin mai nagarta. Ya ce ba zai yi watsi da kyakkyawar makomar Jihar Kano ta fuskar ilimi ba, kasancewarsa abu na farko da suke bai wa muhimmanci, san-nan sun gamsu da cewar ilimi ba kawai abin alfahari ga al’umma ba ne har ma da kasancewarsa babban jari da kowa ke iya amfana da yara masu tasowa.

“Jiharmu mai albarka na fuskantar gagarumin kalubalen matsalar yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, kamar yadda kididdiga ta nuna akwai yara 989,234 da ba sa zuwa makaranta.

“Shekara guda da ta gabata ta kasance cike da kalubale. Makarantunmu da ya kamata su zama cibiyoyin ilimi, yanzu haka suna cikin wani mummunan yanayin a Jihar Kano.

“Rashin isassun kayan karatu sun kara ta’azzara matsalar, inda aka bar malamai da dalibai na ta fama da tsoffin kayan aiki marasa inganci. Sama da dalibai miliyon 4.7 ke zaune a kasa wajen daukar darasi.”

Haka kuma gwamna ya sanar da bude wasu makarantun kwana da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta rufe a fadin Jihar Kano.

People are also reading