'Yan Bindiga Sun Tare Hanyar Kaduna Zuwa Abuja, Sun Sace Fasinjoji Masu Yawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da dama bayan sun buɗe wuta kan wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 a kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar ne a mahaɗar Bishini, kusa da Katari a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Wani mazaunin Katari mai suna Saleh Ibrahim ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Litinin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saleh Ibrahim ya ce ƴan bindigan sun fito daga daji ne a wata lanƙwasa sannan suka buɗe wuta kan motar bas ɗin da ke jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce ƴan bindigar sun harbi tayoyin motar bas ɗin wanda hakan ya tilastawa motar ta kauce daga kan hanyar zuwa cikin daji, kafin daga bisani suka tasa dukkanin fasinjojin zuwa cikin daji.
Ya kuma ƙara da cewa, ƴan bindigan sun yi awon gaba da fasinjojin wasu motoci guda biyu.
"Babban abin ban haushi shi ne, wurin da lamarin ya faru tun daga mahaɗar Bishini zuwa inda sojoji suka sanya shingen bincikensu bai wuce kilomita ɗaya ba."
- Saleh Ibrahim
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba kan sace fasinjojin da ƴan bindiga suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Hassan Mansur, domin samun ƙarin bayani, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum 22 a ƙauyukan Gidan Bofa da Dan Nakwabo a ƙaramar hukumar Kankara ta jihar.
Ƴan bindigan sun kuma kashe jami’an ƴan sanda mutum huɗu da suka haɗa da sufeto uku da kofur ɗaya tare kashe wasu jami'an rundunar KSWC mutum biyu.
Asali: Legit.ng