Home Back

Dakarun Sojojin Nijeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 5 Sun Kuɓutar Da Wasu A Sokoto

leadership.ng 3 days ago
Dakarun Sojojin Nijeriya Sun Kashe Ƴan Ta’adda 5 Sun Kuɓutar Da Wasu A Sokoto

Dakarun Sojojin Najeriya sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a jihar Sokoto a yau Alhamis, inda suka kashe ‘yan ta’adda biyar tare da kuɓutar da wasu mutane biyu da suka yi garkuwa da su a mummunar musayar wuta da aka yi.

Artabun dai ya faru ne a dajin Baniguntu da Gohonau da ke ƙaramar hukumar Gudu, lamarin da ya yi sanadiyar kashe ƴan bindigar, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga.

Mutanen da aka kuɓutar da su, Nura Isya da Saluhu Hamza, an mika su cikin ƙoshin lafiya ga shugaban karamar hukumar Gudu domin kula da lafiyarsu tare da sake haɗuwa da iyalansu.

Bayan artabun Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar, alburusai 32, da wayar Tecno, hakan ya taimaka wajen daƙile ayyukan ƙungiyar ta’addancin a yankin.

Sanarwar da Rundunar Sojin Najeriya ta fitar ta bayyana wannan aiki a matsayin wata shaida da ke nuna aniyarsu ta yaƙi da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro da tsaron al’umma a Jihar Sakkwato da ma faɗin ƙasar nan.

Matakin da sojojin suka ɗauka cikin gaggawa na nuna jajircewarsu wajen kare rayuka da walwalar mutanen da suke yi wa aiki.

People are also reading