Sarautar Kano: Kungiyar Lauyoyin Arewa Ta Fadi Sahihin Sarkin Kano Bayan Yanke Hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Kungiyar lauyoyi a Arewacin Najeriya (NCNLPIA) ta sake magana kan dambarwar sarautar Kano.
Kungiyar ta ce Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano a yanzu bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya.
Lauyoyin suka ce hukuncin ya tabbatar da saɓa doka da Gwamna Abba Kabir ya yi wajen rusa masarautun jihar guda biyar, cewar Daily Trust.
Shugaban kungiyar, Barista Napoleon Otache ya yabawa kotu kan hukuncin da ta yi na adalci.
"Rusa matakan Gwamna Abba Kabir da kotun ta yi ya tabbatar da cewa a yanzu kotu ne gatan talaka a Najeriya."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Muradun al'umma sune kan gaba da komai kuma wadanda ke da gaskiya ba su bukatar tayar da hankula domin tabbatar da ƴancinsu."
- Napoleon Otache
A wani labarin, kun ji cewa lauya Abba Hikima ya magantu kan sahihin Sarkin Kano yayin da ake ci gaba da dambarwar.
Hikima ya ce Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano idan aka yi duba a mahangar shari'a da dokar kasa.
Wannan na zuwa ne bayan yanke hukunci da Babbar Kotun Tarayya ta yi a jihar kan rigimar sarautar jihar.
Asali: Legit.ng