Home Back

"Mataimakin gwamna a Najeriya kamar ba ka da aiki ne"

bbc.com 2024/6/30

"Mataimakin gwamna a Najeriya kamar ba ka da aiki ne"

Minti 1 da ta wuce

Wani tsohon ministan lantarki kuma tsohon mataimakin gwamna a jihar Yobe, ya ce babban sirrin zama mataimakin gwamna da gwamna shi ne gaskiya da riƙon amana da kuma biyayya.

Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce duk da yake tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi muƙamin mataimakin gwamna, amma kuma bai tanadar masa wani taƙamaiman aiki ba, don haka “in dai kana so ka yi, ka zauna kawai. Abin da gwamna ya ce ka yi, ka yi. In ya ce kar ka yi, ka bari”.

A cewarsa: “Ba zancen kai deputy gwamna (ne), ai tare muka je mu kai kamfen, ai tare muka je... Ai gwamnatin, tsarin mulki ne yake ajiye ta, to kai kuma tsarin mulki ba abin da ya ba ka”.

Yana wannan jawabi ne a wani ɓangare na jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya albarkacin cikar mulkin dimokraɗiyya shekara 25 karon farko a tarihin ƙasar.

Da aka tambaye shi, ko yana jaddada maganar nan da wasu ta yaɗawa ce a ƙasar ta cewa mataimakin gwamna daidai yake da matsayin safaya taya, sai Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ƙyalƙyale da dariya, yana cewa: “Wanda ya ƙirƙiro (maganar) safaya taya ɗin nan ya yi ƙoƙari, amma ni dai ban ce haka ba”.

Ya kuma bayyana ra’ayinsa kan ci gaba ko akasin haka da yake gani an samu a tsawon shekara 25 na mulkin jamhuriya ta huɗu, wadda ya ce a ganinsa ci gaban da aka samu bai kai na zamanin jamhuriyar ta farko ba wadda kwata-kwata ba ta fi shekara shida ba.

People are also reading