Home Back

Me rusa Majalisar Yaƙi ta Isra'ila da Netanyahu ya yi ke nufi?

bbc.com 2024/7/1
..

Asalin hoton, EPA

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya rushe Majalisar Yaƙin ƙasar mai mutum bakwai, wani mataki da ake kyautata zaton ba zai rasa nasaba da ficewar da ɗan siyasar nan mai tsattsauran ra'ayi na jam'iyyar adawa, Gadi Eisenkot ya yi daga majalisar ba.

Kafafen watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa yanzu duk manyan batutuwan da suka shafi yaƙin da isra'ila ke yi da Hamas a Gaza za a rinƙa tattauna su ne a wani yanayin da bai kai majalisar yakin da aka rusa ba.

Tun bayan ficewar mista Gantz - kwana takwas da suka gabata - kan abin da ya kira rashin tsari mai kyau na yaƙi, ake ta samun kiraye-kiraye ga ministoci masu ra'ayi irin nasa da su maye gurbinsa.

Rushe majalisar tsaron na nufin Mista Netanyahu ya kauce wa sammatsi da dabarun siyasa na abokan haɗakarsa da kuma ƙawayen Isra'ila na waje.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila da ke yaƙi a Gaza ta IDF, ya ce a iya sanin su babu abin da zai shafi yadda tsarin samun umarni dangane da yaƙi zai ci gaba da kasancewa.

Shi dai Mista Gantz da mista Eisenkot sun shiga gwamnatin haɗaka ne tare da ɓangaren Benjamin Netanyahu na masu ra'ayin mazan jiya bayan fara yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza tun watan Oktoba.

Mutanen biyu waɗanda sun taɓa shugabantar rundunar ta Isra'ila mai yaƙi a Gaza, IDF, sun sanar da murabus din nasu ne ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma shi mista Gantz ya ce salon mulkin firaiminista Benjamin Netanyahu "na hana su cimma nasara ta haƙika".

Kuma jim kaɗan bayan murabus ɗin, ministan tsaron kasar mai ra'ayin riƙau, Itamar Ben-Gvir ya ce ya rubuta wa mista Netanyahu wasiƙa domin neman ya sanya sunansa a majalisar yaƙin.

A daren Lahadi ne kuma mista Netanyahu aka rawaito cewa ya sanar da ministocinsa cewa ya yanke ƙudirin rushe majalisar yaƙin maimakon ya zuba sababbin mambobinta.

"An kafa Majalisar yaƙin ne a matsayin yarjejeniyar Gantz na shiga gwamnatin haɗaka. Kuma yana fita babu buƙatar ci gaba da majalisar," Netanyahu ya ce kamar yadda jaridar Jerusalem Post ta rawaito.

Wane tasiri hakan ke da shi ga yaƙi a Gaza?

..

Jaridar Haaretz ta rawaito cewa wasu daga cikin waɗanda aka tattauna kansu a majalisar yanzu za a miƙa su ne domin ci gaba da tattaunawa ga wata majalisar tsaro mai mutum 14 wadda ta kunshi Mista Ben-Gavir da kuma ministan kudin kasar, Bezala Smotrich mai tsattsauran ra'ayi.

Mai magana da yawun rundunar IDF, Daniel Hagari ya dage kai da fata a ranar Litinin cewa abin da ke faruwa ba zai shafi ayyukan rundunar ba.

Akwai alamu da ke nuna gwamnatin Isra'ila na fuskantar ƴar gajiyawa a ƴan kwanakin da suka gabata, inda mista Netanyahu da ministocinsa masu ra'ayin riƙau suke sukar ayyukan rundunar IDF na kokarin fito da "tsagaita wuta" da rana a kusa da Rafah domin bayar da damar shigar da kayan agaji.

Ƙwarya-ƙwaryar tsagaita wutar dai na nufin barin motocin su ɗauki kayan agaji domin shiga da su wuraren da Isra'ila ke iko da su kamar Karem Shalom da ke kan mashigar Rafah da kuma zuwa titin arewa maso kudancin Gaza. An dai hana shigar kayan agajin ne zuwa Rafah tun watan da ya gabata lokacin da dakarun Isra'ila suka fara kai hare-hare a mashigar.

To sai dai Mista Ben-Gvir ya koka cewa tsarin "wauta" ne, inda ita kuma kafar watsa labarai ta Isra'ila ta rawaito Netanyahu na cewa " Muna da ƙasa da ke iko da dakaru ba dakarun da ke iko da ƙasa ba."

Ita kuma rundunar ta IDF ta mayar da martani cewa tsagaita wutar ba ya nufin za a dakata da artabun da ake yi a kudancin Rafah, wani abu da ya haifar da ruɗani dangane da haƙiƙanin abin da ke faruwa a fagen.

Hukumar 'Yan gudun hijra ta Falasdinu, Unrwa wadda ita ce babbar ƙungiyar agaji a Gaza, ta rawaito cewa artabu na ci gaba a Rafah da sauran wurare a kudanci a ranar Litinin sannan kuma "babu abin da ya sauya dangane da yaƙin har yanzu".

Rundunar IDF ta ce dakarunta na " ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da bayanan sirri suka tabbatar a Rafah". Ta kuma ƙara da cewa sun gano wasu wuraren da makamai da abbubuwan fashewa sannan sun kashe "ƴan ta'adda da dama a yankin Tal al-Sultan.

Alamu na nuna cewa akwai haske dangane da cimma cikakkiyar tsagaita wuta a Gaza, an kuma samu karin gargadi daga sojojin Isra'ila cewa rikicin da ke faruwa tsakanin Hezbollah da Isra'ila shi ne ke barazanar ɓarkewa zuwa gagarumin yaƙi.

Sakamakon ƙara ƙaimin musayar wutar da ya ƙaru a baya-bayan nan, wani babban jami'in diflomasiyya na Amurka na yin bulaguro zuwa yankin domin ganin an shiga tsakani domin kashe wutar da ke ruruwa a kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

People are also reading