Home Back

Shugaban EFCC Ya Koka Kan Girman Satar da Ake Yi, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi

legit.ng 2 days ago
  • Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da masu aikata rashin gaskiya ya koka kan irin girman satar da ake yi a ƙasar nan
  • Ola Olukoyede ya bayyana cewa wasu lokutan yana mamakin yadda ƙasar nan har yanzu ba ta ruguje ba idan ya yi arba da wasu takardun shari'a kan satar da aka yi
  • Shugaban na EFCC ya kuma ƙara da cewa da ƴan Najeriya za su ga irin girman satar da ake yi, da sun zubar da ƙwalla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, Ola Olukoyede, ya koka kan girman satar da wasu masu cin hanci da rashawa ke yi a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa ya kan kasance a cikin mamaki kan yadda har yanzu ƙasar nan ba ta durƙushe ba duk lokacin da ya duba takardun shari'a ya ga irin kuɗaɗen da aka sata.

Shugaban EFCC ya koka kan cin hanci a Najeriya
Shugaban EFCC ya koka kan satar da ake yi a Najeriya Hoto: @OfficialEFCC Asali: Facebook

Ola Olukoyede ya ƙara da cewa da ƴan Najeriya za su ga wasu daga cikin takardun shari'ar da sun zubar da ƙwalla.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me shugaban EFCC ya ce kan sata a Najeriya?

A cewar wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Talata a shafin X, shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin hukumar RMAFC.

"A lokacin da na duba wasu takardun shari'a na ga irin maƙudan kuɗaɗen da aka sace, ina mamakin yadda har yanzu ƙasar nan take raye. Idan ka ga wasu takardun dole a zubar da ƙwalla."
"Za ka rasa wane irin hali mu ƴan Najeriya muke da shi duba da yadda suke tura ragowar kuɗaɗen kasafin kuɗi da ba a kashe ba zuwa asusun banki kafin tsakar dare a ƙarshen kasafin kuɗi."

- Ola Olukoyede

Ya kuma bayyana cewa cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikatan gwamnati shi ne mafi girman cin hanci a Najeriya.

Ya yi nuni da cewa idan aka kawar da cin hanci a ɓangaren gwamnati, ƙasar nan za ta yiwa ƙasashen duniya masu yawa fintinkau wajen ci gaba.

Jami'in EFCC ya kashe kansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami’in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ya yanke shawarar barin duniya.

Jami'in na hukumar EFCC ya salwantar da ransa ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading