Shugaban EFCC Ya Koka Kan Girman Satar da Ake Yi, Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, Ola Olukoyede, ya koka kan girman satar da wasu masu cin hanci da rashawa ke yi a ƙasar nan.
Ya bayyana cewa ya kan kasance a cikin mamaki kan yadda har yanzu ƙasar nan ba ta durƙushe ba duk lokacin da ya duba takardun shari'a ya ga irin kuɗaɗen da aka sata.
Ola Olukoyede ya ƙara da cewa da ƴan Najeriya za su ga wasu daga cikin takardun shari'ar da sun zubar da ƙwalla.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Talata a shafin X, shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin hukumar RMAFC.
"A lokacin da na duba wasu takardun shari'a na ga irin maƙudan kuɗaɗen da aka sace, ina mamakin yadda har yanzu ƙasar nan take raye. Idan ka ga wasu takardun dole a zubar da ƙwalla."
"Za ka rasa wane irin hali mu ƴan Najeriya muke da shi duba da yadda suke tura ragowar kuɗaɗen kasafin kuɗi da ba a kashe ba zuwa asusun banki kafin tsakar dare a ƙarshen kasafin kuɗi."
- Ola Olukoyede
Ya kuma bayyana cewa cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikatan gwamnati shi ne mafi girman cin hanci a Najeriya.
Ya yi nuni da cewa idan aka kawar da cin hanci a ɓangaren gwamnati, ƙasar nan za ta yiwa ƙasashen duniya masu yawa fintinkau wajen ci gaba.
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami’in hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ya yanke shawarar barin duniya.
Jami'in na hukumar EFCC ya salwantar da ransa ne a gidansa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2024.
Asali: Legit.ng